Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya 292 sun sauka daga kasar Saudi Arabia

Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya 292 sun sauka daga kasar Saudi Arabia

Gwamnatin tarayya ta kwaso 'yan Najeriya 292 daga kasar Saudiyya sakamakon annobar COVID-19.

Jirgin da ke dauke da 'yan Najeriyan ya iso ne a daren Talata kuma ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

A safiyar Laraba ne ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya sanar da hakan ta shafinsa na twitter.

Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya 292 sun sauka daga kasar Saudi Arabia
Yanzu-yanzu: 'Yan Najeriya 292 sun sauka daga kasar Saudi Arabia
Asali: Original

"Mun karba 'yan Najeriya 292 daga kasar Saudiyya a jiya. Gwamnatin kasar Saudiyya din ce ta dawo dasu har zuwa Abuja. Da yawa daga cikinsu mata ne masu shayarwa sai kuma kananan yara.

"Mun killacesu a otal don kwashe kwanaki 14 kamar yadda hukumar kiwon lafiya ta duniya ta shardanta," yace.

A kokarin gwamnatin tarayyar na kwaso 'yan kasarta da ke kasashen ke tare, a kalla 'yan Najeriya 300 ne suka iso gida daga Ingila a makonni biyu da suka gabata, gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya bada umarnin sakin albashin watan Mayu na ma'aikatan jihar

A gefe guda, ministan kiwon lafiya a gwamnatin Buhari, Osagie Ehanire ya ce gwamnati ta damu kwarai da yadda manyan mutane masu ilimi ke mutuwa dalilin cutar Coronavirus.

Punch ta ruwaito ministan ya bayyana dalili, inda yace masu kudin sun gwammace a kula dasu a gidajensu a kan su tafi cibiyoyin kulawa da masu cutar, sai lamari ya baci ake kai su asibiti.

Osagie ya bayyana haka ne yayin taron manema labaru da kwamitin yaki da COVID-19 a Najeriya ta shirya a garin Abuja, a ranar Talata, inda ya baiwa masu dauke da cutar shawara.

Ministan ya yi kira a garesu dasu bi umarnin likitoci wajen shan magani ba son ran su ba.

A yanzu haka cibiyoyin bincike 5 suna aiki a kan magungunan COVID-19, daga cikinsu har da Chloroquine.

Daga karshe ministan yace suna aikin zagayen cibiyoyin killace masu cutar, zuwa yanzu sun je Yenagoa a jahar Bayelsa da Osogbo na jahar Osun State, kuma zasu cigaba da taimaka musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng