Mutanen arziki sun taimakawa Sani Adamu da makudan kudi da kayan bikin sallah

Mutanen arziki sun taimakawa Sani Adamu da makudan kudi da kayan bikin sallah

Idan ba ku manta ba a ranar Talata mu ka kawo maku rahoto wani tsohon da ya fito ya na neman taimako. Wannan mutumi ya yi aiki da shugaba Muhammadu Buhari a shekarun baya.

Sani Adamu mai ritaya ya kawo kuka gaban Duniya cewa karfinsa ya kare, kuma kudinsa na gidan soja ba su fito ba, don haka ya roki shugaban Najeriya da iyalinsa su kawo masa agaji.

A halin yanzu har Ubangiji ya fara amsar addu’ar wannan dattijo. Wasu bayin Allah masu tausayi sun kai masa ziyara, kuma sun yi masa abin-a-yaba, inda su ka ba shi kayan cin sallah.

Kamar yadda mu ka gani a wani bidiyo da wani daga cikin hadiman shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa, ta’alikin ya samu kyautar kudi da mu ke tunanin sun kai N100, 000.

Malam Bashir Ahmaad ya ce wani bawan Allah wanda ake kira @DanBorno a shafin Tuwita, shi ne ya gano inda wannan mutumi ya ke, ya kai masa wannan gagarumar gudumuwa.

KU KARANTA: Sani Adamu mai ritaya ya sake aikowa Buhari wani bidiyon neman agaji

Bayan haka an taimakawa wannan tsohon jami’in soja da huluna biyu na fitar shari’a. Haka zalika Sani Adamu ya samu kyautar shaddoji na kece-raini wanda zai ci bikin sallah da su.

Daga cikin rigunan da aka ba Sani Adamu mai ritaya, har da babbar riga wanda ta sha aiki. A karshe ya yi godiya sosai, ya kuma yi addu’ar karin arziki ga wadanda su ka taimaka masa.

Ahmaad ya nuna cewa kadan kenan daga cikin alherin da Adamu zai samu. Hadimin shugaban kasar ya ce nan gaba wasu kayan za su biyo, ya kuma godewa wanda ya fito da bidiyon.

Sani Adamu ya ce ya yi aiki da shugaban kasar na tsawon shekara takwas, tun ya na sabon shiga aikin soja a 1964. Adamu ya kasance direban 'ya 'yan Buhari a lokacin da ya ke gwamna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel