Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin Sheikh Ahmed Lemu

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin Sheikh Ahmed Lemu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan Sheikh Ahmed Lemu na rasuwar babbar dansa, Abubakar Shehu Lemu.

A cikin jawabin da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, shugaba Buhari ya mika sakon ta'aziyyarsa ga ilahirin mutanen jihar Neja bisa rashin da ya kira da 'wanda ba za a maye gurbinsa ba'.

A cikin sakon, Buhari ya ce, amadadinsa tare da iyalinsa, ya na taya Sheikh Lemu jimamin rashin da ya yi.

"Na san tilas za ka kasance cikin radadin rashin babban yaronka," kamar yadda ya kara da cewa.

Ya roki Allah ya bawa Sheikh Lemu da iyalinsa hakurin jure rashin da ya samesu tare da rokawa mamacin rahamar Ubangiji.

Marigayi Abubakar, darekta a ma'aikatar harkokin kasashen waje, ya mutu bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin Sheikh Ahmed Lemu
Buhari
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa da safiyar ranar Talata, ta sanar da cewa sanannen malami kuma shugaban majalisar limaman jihar Kano, Falalu Dan Almajiri, ya rasu.

Marigayin limamin ya rasu ne a sa'o'in farko na yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020.

DUBA WANNAN: 'Ki tuba' - Pantami ya yi wa matashiya wa'azi bayan ta kira shi da 'Dan aljannah'

A watan Nuwamban 2018, Dan Almajiri ya yi murabus a matsayin shugaban majalisar zartarwa ta hukumar walwalar alhazan jihar Kano, sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.

Tun daga bullar annobar korona a kasar nan, ana ci gaba da fuskantar mace-mace a jihar Kano ballantana a tsakanin dattawa.

Duk da har yanzu a hukumance babu wata alaka da ta danganta mace-macen da annobar, akwai zargi mai matukar karfi da ke dangana hakan da cutar COVID-19 a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel