Bidiyon yadda ma su jinyar korona ke raha da wasan 'yar wulliya a cibiyar killacewa a Abuja

Bidiyon yadda ma su jinyar korona ke raha da wasan 'yar wulliya a cibiyar killacewa a Abuja

Wani faifan bidiyo da wani dan Najeriya mai suna @darealsimple ya wallafa a shafinsa na tuwita ya nuna yadda wasu ma su jinyar cutar korona a cibiyar killacewa da ke Gwagwalada a Abuja ke raha da wasa abinsu, kamar ba marasa lafiya ba.

A cikin faifan bidiyon, an ga ma su jinyar, yawancinsu matasa maza, na wasa da raha tare da fallewa da gudu a cikin wani dogon daki da aka killace su.

Babu wata alama da ke nuna cewa ma su jinyar na cikin yanayi na rashin koshin lafiya, hasali ma, wasan 'yar wulliyar da su ke yi ba kowanne mai koshin lafiyane zai iya ba.

A cikin faifan bidiyon, mai tsawon dakika tara, za a iya jin ma su jinyar na magana cikin yaren Hausa tare da kyalkyala dariya a yayinda su ke wasa a cikin dakinsu da ke cibiyar killacewar.

A ranar Talata ne aka wayi gari da kwarmata korafin a kawo karshen damafara da sunan korona a Najeriya a dandalin sada zumunta na tuwita.

A ranar Litinin ne daya daga cikin ma su jinyar korona da aka sallama daga cibiyar killacewa a jihar Delta ta yi zargin cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya.

Matar, mai shekaru 36, ta kamu da cutar korona a ranar 17 ga watan Afrilu bayan an yi jayayya da ita a kan sakamakon gwajin kwayar cutar da aka yi mata.

Daga bisani an dauketa zuwa cibiyar killace ma su cutar korona da ke garin Warri, inda ta shafe kwanaki 17 ta na jinya kafin daga karshe a sallameta.

DUBA WANNAN: 'Ki tuba' - Pantami ya yi wa matashiya wa'azi bayan ta kira shi da 'Dan aljannah'

Yayin ganawarta da manema labarai bayan an sallameta, matar ta kafe a kan cewa damfara kawai ake yi da sunan cutar a Najeriya, saboda har yanzu ba ta ga sakamakonta da ya nuna cewa ta na dauke da kwayar cutar ba.

"Ta sakon radiyo aka sanar da ni cewa na kamu da cutar. Kira na aka yi aka sanar da ni ba tare da bani wani rubutaccen sakamako ba. Tun kafin su tafi da ni cibiyar killacewa na sanar da su cewa babu kwayar cutar a kasar nan," kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito matar na fada.

"Ba za a iya shawo kan cutar ba idan da gaske akwai ta a kasar nan. Watakila akwai ta a nahiyar Turai, amma babu ita a nan. An ajiyeni a cibiyar killacewa ba tare da amincewa ta ba.

"Har yanzu ana cigaba da samun cunkuso a kasuwanni da bankuna, idan da gaskene cutar ta shigo kasar nan da mutane da yawa sun kamu. Damfara ake yi da sunan cutar a Najeriya.

"Ni shaida ce, na je kuma na gani. Ban yarda na kamu da cutar korona ba duk da an kai ni cibiyar killacewa a matsayin mai jinya.

"Abokina da mu ke zaune tare kafin a kai ni cibiyar killacewa ya cigaba da rayuwarsa a gida. Sakamakon gwaji bai nuna ya kamu da cutar ba. Ina batun sauran dangina da mu ke tare a gida?

"Mahaifiyata ce ke min wanka, sannan ta kwana tare da ni lokacin da bani da lafiya. Shekarar mahaifiyata 70 a duniya, amma duk da irin kusancinmu ba ta kamu da cutar ba, ta cigaba da rayuwarta a gida.

"Ba su shirya wasan kwaikwayon ba sosai su amma su ka fara nuna shi. Kamata ya yi su binciki dukkan iyalina. Hatta Sakamakon da ake yadawa a kan cewa likitocin da ke duba lafiyata sun kamu da cutar duk karyane, shirya abin su ka yi," a cewar matar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel