Dan tsaro ba tsoro ba: Gwamnati ta girke zaratan Sojoji masu jiran ko-ta-kwana a jahar Filato

Dan tsaro ba tsoro ba: Gwamnati ta girke zaratan Sojoji masu jiran ko-ta-kwana a jahar Filato

A kokarinta na magance matsalolin tsaro da suka addabi jahar Filato, gwamnatin tarayya ta tura kwararrun dakarun Soji na musamman guda 35 zuwa jahar.

Punch ta ruwaito Sojojin sun isa Filato da misalin karfe 8:50 na safe ne cikin jirgin rundunar Sojan sama, kai tsaye suka zarce sansanin Sojan sama na 205 combat search and rescue.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika ma majalisa sunan Yuguda don nada shi muhimmin mukami

Kwamandan sansanin dake cikin karamar hukumar Mangu, Air Commodore Eimobo O. Ebiowe ne ya tarbe su a karkashin jagorancin kwamandansu, Air Vice Marshal Charles Ohwo.

Dan tsaro ba tsoro ba: Gwamnati ta girke zaratan Sojoji masu jiran ko-ta-kwana a jahar Filato
Sojoji Hoto: Punch
Asali: UGC

A jawabinsa, kwamandan Sojojin, Charles, ya bayyana cewa suna daga cikin kwararrun Sojoji 94 masu kai agaji da babban hafsan sojan sama, Sadique Abubakar ya horas da kansa.

“Mun kawo su jahar Filato ne don su karfafa tsaro a jahar bayan sun kammala samun horo, kwararrun Sojoji wanda suka samu karin horo akan yaki, bincike da kuma kai dauki.

“A duk inda aka samu tashin tashina ko na yan bindiga, ko rikicin manoma da makiyaya ana sa ran zasu kwantar da tarzomar, sa’annan su koma sansaninsu.” Inji shi.

Daga karshe ya bayyana tabbacinsa game da kokarin da ake yi na samar da zaman lafiya a jahar, inda yace hakan su zai cimma ruwa.

A wani labari kuma, wasu gungun miyagu yan bindiga sun kashe akalla mutane 10 yayin wasu jerin hare hare da suka kai a kauyukan Kajera da Maguzawa na jahar Zamfara.

Yan bindigan sun kaddamar da hare haren ne a karamar hukumar Tsafe a daren Talata, inda suka dinga bi suna bindige mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Haka zalika, wakilin mazabar Sakkwato ta gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gobir ya bayyana cewa Sojojin Najeriya ba su iya kare jama’ansa daga harin yan bindiga.

Gobir ya bayyana haka ne a ranar Talata, 19 ga watan Mayu yayin zaman majalisar, inda yace a yanzu haka Sojojin kasar Nijar ne ke taimakon jama’a tare da fatattakar yan bindigan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel