Miyagu sun kai farmaki kauyukan Zamfara, sun kashe mutane 10

Miyagu sun kai farmaki kauyukan Zamfara, sun kashe mutane 10

Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kashe akalla mutane 10 yayin wasu jerin hare hare da suka kai a kauyukan Kajera da Maguzawa na jahar Zamfara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yan bindigan sun kaddamar da hare haren ne a karamar hukumar Tsafe a daren Talata, inda suka dinga bi suna bindige mutanen da basu ji ba basu gani ba.

KU KARANTA: Abin da yasa Malaman Jami’a 1,180 basu samu albashin su ba – Babban akanta Ahmad

Wani mazaunin guda daga cikin kauyukan mai suna Mustapha ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace:

“Sun bude ma jama’a wuta a kauyukan nan inda suka kashe mutane 10, daga nan suka tsere, mun gawarwakinsu daga bisani, muka binne su a kauyen Magazu.

“Shugaban karamar hukumar Tsafe ne ya tattaro jama’a daga ciki har da yan banga wanda suka taimaka wajen dauko gawarwakin, saboda ana tsoron yan bindigan za su iya dawowa don su hana sallar jana’izar.” Inji shi.

Miyagu sun kai farmaki kauyukan Zamfara, sun kashe mutane 10

Gwamnan Zamfara Hoto: Twitter
Source: Twitter

Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin kakaakin rundunar Yansandan jahar Zamfara, SP Muhammad Shehu game da lamarin ya ci tura sakamakon baya amsa wayansa.

A yan kwanakin nan an samu karuwar hare haren kungiyoyin miyagu yan bindiga a jahohin Zamfara, Katsina, Sakkwato da wasu sassan yankin Arewa maso yammacin Najeriya.

A wani labarin kuma, wakilin mazabar Sakkwato ta gabas a majalisar dattawa, Sanata Ibrahim Gobir ya bayyana cewa Sojojin Najeriya ba su iya kare jama’ansa daga harin yan bindiga.

Gobir ya bayyana haka ne a ranar Talata, 19 ga watan Mayu yayin zaman majalisar, inda yace a yanzu haka Sojojin kasar Nijar ne ke taimakon jama’a tare da fatattakar yan bindigan.

“Jama’a na basu da tsaro da aminci, saboda yawan hare haren yan bindiga, akalla mutane 300 sun mutu ko aka sace su a cikin watanni uku da suka gabata, an sace shanu 5,780 da darajarsu ta haura naira biliyan 2.5” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel