An kashe mutum 8000 cikin shekaru 10 a Arewa maso Yamma - ICG
Wani hasashe ya nuna sakamakon rashin tsaro da ake fama da shi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, mutane kimanin 8, 000 su ka mutu a shekaru goman da su ka wuce.
Kungiyar ICR ta bayyana cewa bayan mutane 8, 000 da su ka rasa rayuwarsu a dalilin rashin tsaro a yankin, an tarwatsa kusan mutane fiye da 260, 000 daga gidajensu a wannan lokaci.
A wani rahoto da wannan kungiya mai suna International Crisis Group ta fitar kwanan nan a shafinta na yanar gizo, ta ce jihar Zamfara ce gaba wajen fama da matsalar rashin tsaro.
Mutane 60, 000 aka raba da gidajensu a shekaru goman nan da su ka wuce. Taken wannan sabon rahoto da aka fitar shi ne: “Rikici a arewa maso yamma: Komawa cikin hayaniya”
Kungiyar mai zaman kan-ta ta ce wadannan mutane da aka fatattaka su na gudun hijira. Daga cikin wadanda aka raba da gidajensu, akwai mutum 60, 000 da su ka fake a kasar Nijar.
KU KARANTA: Gwamnati ta nada sabon Shugaban Jami’ar Tarayyar Katsina
A dalilin rashin tsaron da ake fama da shi a yankin, an yi asarar dabbobi da abinci. Wannan ya jawo makiyaya sun tsere sun koma arewa maso tsakiya da kuma kudancin kasar.
Hijirar makiyaya ya jawo yawan sabanin da ake samu tsakanin makiyayan da manoma a jihohin arewa ta tsakiya. Binciken ya ce wadannan kashe-kashe ya fi tasiri ne kauyuka.
ICR ta ce an kuma samu karuwar garkuwa da mutane a jihohin Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara. A kan tsare jama’a a karbi kudin fansa a hannunsu.
A rahoton kungiyar, ta ba hukumomi shawarar yadda za a kawo karshen wannan matsala na kashe jama’a da garkuwa da mutane ta hanyar baza jami’an tsaro a jihohin shiyyar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng