Yanzu-yanzu: Mai korona ta haifi tagwaye a Legas (Hoto)

Yanzu-yanzu: Mai korona ta haifi tagwaye a Legas (Hoto)

Wata mata mai shekaru 22 cikin wadanda suke jinyar COVID-19 a Legas ta haifi tagwaye a Asibitin Koyarwa ta Jamiar Legas (LUTH).

Mai jinyar ta haifi mace da na miji a ranar Talata 19 ga watan Mayu, hakan ya kawo jimillar jariran da aka haifa a asibitin zuwa hudu.

Asibitin ya tabbatar da haihuwar tagwayen cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Twitter.

Sakon ya ce, "Tawagar likitoci a LUTH da masu kula da numfashi da jamian jinyan a yau Talata, 19 ga watan Mayun 2020 sun taimakawa wata mata mai shekaru 22 da ke dauke da COVID-19 ta haifi tagwaye mace da na miji.

"Nauyin jariran a lokacin da aka haife su kilogram 3.2 na miji sai macen kilogram 3.25, matar ta haihu ne ta hanyar tiyata.

"Mahaifiyar da jariran duk suna cikin koshin lafiya!”.

Ga ainihin sakon a kasa:

DUBA WANNAN: COVID-19: An kama Janar din Soja da malamin addinin musulunci a Kaduna

A wani rahoton, kunji cewa 'yan bindiga tara ne suka rasa rayukansu sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan sa kai a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Al'amarin ya faru ne a kauyukan Karaya Mahanga da Bakachi da sa'o'in farko na ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun yi artabu da 'yan sanda da kuma 'yan sa kai a kauyen Mekujeri da ke kusa da Kagara ta karamar hukumar Rafi ta jihar.

Ya ce DPO din Kagara ya gaggauta tura rundunar Operation Puff Adder tare da wasu 'yan sa kai wadanda suka dinga ruwan wuta da 'yan bindigar da suka dade suna gallabar jama'ar Rafi da kewaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel