'Ki tuba' - Pantami ya yi wa matashiya wa'azi bayan ta kira shi da 'dan aljannah'

'Ki tuba' - Pantami ya yi wa matashiya wa'azi bayan ta kira shi da 'dan aljannah'

Ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya bukaci wata matashiya ta tuba bayan ta kira da shi da dan aljanna a dandalin sada zumunta na tuwita.

Matashiyar, mai suna @Zainabsanimika1 a dandalin tuwita, ta wallafa cewa, "@DrIsaPantami Dan aljanna ne", har sau shidda a sahfinta.

Da ya ke mayar da martani a kan kalaman matashiyar, Pantami ya yi ma ta wa'azi a kan cewa bai halatta a kira wani mutum da 'Dan aljannah' ba, tare da bayyana cewa Allah ne kadai ya san waye Dan Allah a yayin da jama'a ke kokarin samun shigarta.

"Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! bai halatta a kira wani mutum da Dan Aljannah ba. Mu na kokarin samun shigarta ne kawai, amma Allah ne kadai ya san waye Dan Aljannah. Allah ya hadamu baki daya a gidan Aljanna. Ki tuba, sanna kar ki sake maimaita hakan," a cewar Pantami.

Kalaman matashiyar na zuwa a daidai lokacin da wasu jama'a a dandalin tuwita ke yawan saka karatun Pantami na baya tare da yi ma sa tunin cewa al'amuran tabarbarewar kasa da ya yi ta kiran a gyara, har yanzu su na cigaba da faruwa.

DUBA WANNAN: Korona a Najeriya damfara ce, wasan kwaikwayon da ba a tsara shi da kyau ba - Mai jinyar da aka sallama

Ma su yin hakan na kafa hujja da kalaman Pantami a kan halin rashin tsaro da kasa ta tsinci kanta a lokacin mulkin jam'iyyar PDP, lamarin da wasu ke ganin har yanzu ba ta sauya zani ba, musamman a bangaren kalubalen tsaro.

Sai dai, wasu daga cikin ma su kare Pantami sun bayyana cewa ba zai yi wu yanzu ya fito ya soki gwamnatin da ya ke cikinta ba, saboda ya na tare da shugabannin, a saboda haka zai iya isar da sako garesu ba tare da fitowa kafafen yada labarai ba.

Cacar baki a kan wanna lamari har yanzu ba ta tsaya ba a dandalin tuwita, ma su sukarsa na yi, ma su kare shi ma na yin nasu kokarin wajen fahimtar da jama'a irin kokarin da ya ke yi a kan kujerarsa ta ministan sadarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel