Zargin cin amana: 'Yan sanda sun bazama neman magidancin da ya like al'aurar matarsa da 'sufagilu'

Zargin cin amana: 'Yan sanda sun bazama neman magidancin da ya like al'aurar matarsa da 'sufagilu'

Jami'an rundunar 'yan sanda sun shiga neman wani magidanci ruwa a jallo bayan ya ci zarafin matarsa a ranar Asabar, 16 ga watan Mayu, bisa zargin ta na cin amanarsa.

Rundunar 'yan sanada a Thuraka da ke kasar Kenya ta ce mai laifin ya aikata wannan tabargaza ne a kusa da wani kogi yayin da ya lallaba matarsa da sunan za su yi bulaguro daga kauyensu Marimanti zuwa Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

A yayin da su ka isa daidai kogin Kathita, magidancin, wanda ke rike da zabgegiyar wuka, ya rufe matarsa da duka tare da yi ma ta barazanar zai kasheta da wukar hannunsa idan ba ta tube kayan jikinta ba.

A cewar 'yan sanda, "a yayin da su ka isa kogin Kathita, sai ya umarci matarsa ta tube tsirara tare da fada ma sa dukkan mazan da ta yi lalata da su yayin da ya ke can Nairobi."

Kiprop Rutto, kwamandan 'yan sanda na kudancin Tharaka, ya cigaba da cewa, "bayan ta yi tsirara, sai magidancin ya yi amfani da wuka ya zuba dakakken barkono da gishiri da aka cakuda da albasa sannan ya saka 'sufagilu' ya like al'aurarta.

Zargin cin amana: 'Yan sanda sun bazama neman magidancin da ya like al'aurar matarsa da 'sufagilu'
Zargin cin amana: 'Yan sanda sun bazama neman magidancin da ya like al'aurar matarsa da 'sufagilu'
Asali: Facebook

"Ya kara saka sufagilu a kunnuwa da bakin matarsa kafin daga bisani ya gudu, ya barta a wurin."

Kwamandan 'yan sandan ya bayyana cewa matar ta yi ta maza, ta daure ta tattaka zuwa ofishin 'yan sanda na Marimanti, inda ta shigar da korafin abinda ya faru gareta.

DUBA WANNAN: Korona a Najeriya damfara ce kawai - Mai jinyar da aka sallama

Mista Rutto ya ce an garzaya da matar zuwa asibitin Marimanti, inda ake duba lafiyarta.

Kazalika, ya bayyana cewa rundunar 'yan sanda ta bazama neman magidancin, wanda da ma sanannen mai laifi ne da hukuma ke nema ruwa a jallo.

A cewarsa, za su gurfanar da magidancin a gaban kotu da zarar ya shiga hannun jami'an tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel