Duk da dokar Buhari, Ganduje ya baiwa Kanawa daman sallar Idi da sallar Juma’a

Duk da dokar Buhari, Ganduje ya baiwa Kanawa daman sallar Idi da sallar Juma’a

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa al’ummar jahar Kano daman gudanar da sallolin Juma’a tare da sallar Idi, duk da dokar zaman gida da gwamnatin tarayya ta sanya.

Babban mashawarcin gwamnan a kan harkar watsa labaru, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara ma Kanawa kwanaki 14 a dokar ‘zaman gida’

Yakasai yace gwamnatin ta yanke wannan shawara ne bayan wata doguwar tattaunawa da ta yi da manyan Malamai guda 30 daga bangarorin Musulunci daban daban a fadar gwamnatin.

Duk da dokar Buhari, Ganduje ya baiwa Kanawa daman sallar Idi da sallar Juma’a
Ganduje Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Facebook

Daga karshe gwamnan ya amince da shawarwarin da aka yanke wurin, don haka ya amince za’a cigaba da dokar zaman gida, kuma za’a cigaba da dage dokar a ranakun Litinin da Alhamis.

Haka zalika gwamnatin ta bada izinin a bude Masallatan Juma’a a duk mako, kuma a gudanar sallar Idi a karamar sallar bana, amma da sharudda kamar haka;

i- Duk wanda zai shiga Masallacin Juma’a sai ya sanya takunkumin fuska

ii- Duk wanda zai shiga sai ya wanke hannuwansa da sanitizer

iii- Dole sai an raba sahu a cikin Masallatan

iv – Dole ne a rage tsawon huduba don rage taron jama'a a Masallatan

Daga karshe kuma mahalarta taron sun amince da cewa babu sauran shagulgulan sallah da za’a gudanar, bugu da kari gwamnatin ta kafa kwamiti da za ta yi rabon kayan tsafta ga Masallatan.

Idan za’a tuna, a ranar Litinin, 18 ga watan Mayu ne gwamnatin tarayya ta tsawaita wa’adin dokar ‘ta-baci’ da ta sanya a jahar Kano zuwa makonni biyu masu zuwa.

Shugaban kwamitin shugaban yaki da cutar Covid19 a Najeriya, sakataren gwamnati, Boss Mustapha ne ya sanar da haka inda yace za’a igaba da dabbaka dokar zaman gida a Kano tsawon makonni 2.

Ku biyo mu don samun cikakken rahoton.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel