Yanzu yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara ma Kanawa kwanaki 14 a dokar ‘zaman gida’

Yanzu yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara ma Kanawa kwanaki 14 a dokar ‘zaman gida’

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsawaita wa’adin dokar ‘ta-baci’ da ta sanya a jahar Kano zuwa makonni biyu masu zuwa.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban kwamitin shugaban kasa dake yaki da cutar Coronavirus a Najeriya, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya sanar da haka a ranar Litinin.

KU KARANTA: Jami’an jinya su 70 sun kamu da cutar Coronavirus yayin da suke aiki a Asibitocin Najeriya

Boss ya bayyana haka ne yayin taron manema labaru da kwamitin ke shiryawa a duk rana a Abuja don sanar da yan Najeriya halin da ake ciki game da aikin da take yi.

A ranar 27 ga watan Afrilu ne shugaban kasa ya dage dokar a birnin tarayya Abuja, Legas da kuma Ogun, yayin da ya sanar da dokar tsagaita zirga zirga a duk kasar daga 4 ga watan Mayu.

A wannan rana ne shugaban ya sanar da dokar ta-baci a jahar Kano, tare da hana duk wani tafiya da bai zama dole ba a tsakanin jahohin Najeriya.

Yanzu yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara ma Kanawa kwanaki 14 a dokar ‘zaman gida’
Yanzu yanzu: Gwamnatin tarayya ta kara ma Kanawa kwanaki 14 a dokar ‘zaman gida’
Asali: Original

A jawabin Boss Mustapha, yace: “Shugaban kasa ya amince da daukan wadannan matakai kamar haka;

I – Duk matakan da aka dauka na doka da wadanda aka sassauta ma wa a karon farko zasu cigaba kamar yadda suke, tsawon mako 2 daga karfe 12 na daren Litinin zuwa 1 ga watan Yuni.

Ii – Za’a a zage damtse wajen bayyana wadanda suka kamu, bin sawun wadanda suka mu’amalanta, tare da kulawa dasu.

Iii – Cigaba da dabbaka dokar zaman gida a Kano tsawon makonni 2

V – Rufe duk wasu garuruwan da aka samu hauhawar bullar cutar idan hakan ta kama, tare da raba musu kayan tallafin abinci da kuma sa ido game da halin da ake ciki.

Vi – Cigaba da hada kai da jama’a don wayar da kawunan jama’an gari game da illolin cutar

Da wannan sabon umarni, hakan na nufin Kanawa ba za su gudanar da bikin Sallah ko Sallar Idi ba kenan, kamar yadda makwabtansu, a Kaduna zasu kasance cikin doka a ranar.

A wani labarin kuma, akalla jami’an jinya da unguwar zoma guda 70 ne suka kamu da cutar Coronavirus daga cikin guda 600 da aka yi ma gwaji, inji shugaban kungiyarsu.

Shugaba Abdurrafiu Adeniji ya bayyana haka ne yayin bikin makon tunawa da jami’an jinya, inda yace mambobinsu 1,000 na cikin hadarin kamuwa da cutar, 200 na killace a yanzu haka.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel