Ciwon y'a mace sai y’a mace: Labarin matar dake shayar da jarirai 20 bayan yan ta’adda sun kashe iyayensu
Masu iya magana na cewa ciwon ƴa mace ma ƴa mace ne, babu shakka, don kuwa wata mata ta dauki gabaran shayar da jarirai marayu guda 20 bayan yan ta’addan sun kashe iyayen su mata.
Jaridar The Guardian ta ruwaito Feroza Younis Omar ta sadaukar da kan ta don shayar da jariran da iyayen su suka mutu suka barsu a wani hari da yan ta’adda suka kai asibitin.
KU KARANTA: Yan bindiga sun bindige jarirai 2 da wasu mutane 11 a Asibitin Afghanistan
Idan za’a tuna Akalla mutane 13 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani hari da yan bindiga suka kai wani asibiti dake garin Kabul na kasar Afghanistan, daga ciki har da jarirai 2.
An ruwaito kakaakin ma’aikatan cikin gida, Tareeq Arian ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace asibitin da aka kai harin na masu haihuwa ne.
Yan bindiga uku ne suka far ma asibitin, kuma suka rike asibitin tsawon sa’o’i kafin jami’an tsaro su samu nasarar kashe su duka, sa’annan suka tseratar da jariran dake cikin asibitin.
“Daga cikin wadanda suka mutu akwai mata masu shayarwa, ma’aikatan jinya, da kuma jarirai, mutane 15 sun jikkata, yayin da aka ceto fiye da mutane 100, har da yan kasar waje uku.” Inji Kakaaki Tareeq.
Wannan ne tasa Feroza, wanda take aiki a ma’aikatar tattalin arziki na kasar daukan matakin shayar da duk jaririn da aka kashe iyayensu a wannan mummunan hari.
Wata mata mai suna Khadija ta ce tana jira a gama wanke sabon jaririn da ta haifa don ta rungume shi ne kwatsam sai yan bindigan suka shigo suka bude wuta a kan kowa.
Amma duk da wannan rudanin, Khadija ta ce ta sha da kyar tare da jaririnta, sakamakon boyewa da suka yi a karkashin wani teburi, hayakan da ya turnuke wurin ya hana a gansu.
Asibitin Barchi yana yammacin Kabul ne, yankin da mabiya akidar Shi’an Hazara suka fi yawa, wadanda mayakan kungiyar ISIS ke yawan yi ma barazana da hare hare.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng