Gambari ya nuna rashin jin dadi kan yadda ake amfani da ofisoshin gwamnati ba ta yadda ya dace ba
Tsohon manajan NSE, Lekan Fadina, ya kwatanta sabon shugaban fadar ma'aikatan shugaba Muhammadu Buhari, Ibrahim Gambari da gogaggen dan difulomasiyya.
Bayan mutuwar Abba Kyari, Buhari ya nada Gambari a matsayin sabon shugaban ma'aikatan fadarsa a ranar Laraba da ta gabata.
A wata takarda da Fadina ya rubuta, ya ce ya san Gambari sama da shekaru 30 da suka gabata kuma sun san abubuwa masu tarin yawa game da ci gaban Najeriya.

Asali: Twitter
"Mutum ne mai ilimi, kwakwalwa da lissafi. Gogaggen malami ne, tsohon minista, mai bincike kuma ya yi aiki har a ketare," yace.
"Sanannen mutum ne wanda ake mututuntwa saboda hazakarsa. Masani ne wanda ba a cika samun irinsa ba. Ya tattauna a bangarori da dama da suka hada da hadin kan Najeriya, fadada tattalin arzikin kasa, fadada al'adu, addini da hukuma.
"Ya yarda da cewa kowanne dan Najeriya na da hakki a kan kasarsa kuma dole a mutunta shi. Yana matukar kin amfani da ofisoshin gwamnati ba ta yadda ya dace ba. A mahangarsa, bautawa kasa da mutane shine daidai.
"Ya yarda cewa shugabanni ne za su zama abun koyi ga mabiya. Tattaunawa, sanar da ilimi da kuma tunani na daya daga cikin tushen shawo kan matsaloli.
"Ya aminta da cewa dole ne Najeriya ta zama wani jigo a nahiyar Afrika kuma ta taka rawar gani wajen tabbatar da kasuwanci tsakaninta da sauran kasashen nahiyar."
Fadina ya ce Gambari mutum ne da ke son ganin ci gaban Najeriya ta kowanne fanni.
Ya kara da cewa, Gambari na ganin cewa ilimi tare da fasaha sune makamin shawo kan matsalolin masu saka hannayen jari da sauran al'amuran tattalin arziki.
A gefe guda, kafatanin gwamnonin Najeriya 36 sun yi alkawarin yin aiki kafada da kafada tare da sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari.
Gwamnonin sun bayyana haka ne cikin wata wasikar taya murna da suka aika masa wanda ta samu sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng