'Yan bindiga sun kashe wani dan Kasuwa a Kano

'Yan bindiga sun kashe wani dan Kasuwa a Kano

Mun samu rahoton cewa an kashe wani dan kasuwa kuma mazaunin Gandurawa a karamar hukumar Minjibir ta jihar Kano, Alhaji Rilwan Ali.

Shugaban karamar hukumar, Alhaji Nasiru Kuniya, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa da ya sanya hannu a kai kuma aka gabatar wa manema labarai.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin babban jami'in hulda da al'umma na karamar hukumar, Yahaya Dadinduniya kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Dadinduniya ya ce wasu 'yan bindiga ne suka haura gidan dan kasuwar da misalin karfe 1.30 na daren Asabar, inda suka harbe shi nan take kuma suka tafi da matarsa.

'Yan bindiga
'Yan bindiga
Asali: Twitter

Sanarwar da Alhaji Kuniya ya sanya wa hannu ta bayyana cewa gwamnatinsa za ta hada hannu da dukkanin hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika kuma a gurfanar dasu a gaban kuliya.

KARANTA KUMA: Sharudan shiga Itikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan

Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi alkawarin cewa rundunar za ta saki cikakken bayani kan gaskiyar abin da ya faru nan ba da jimawa ba.

Ya kuma ba da sanarwar cewa, an kama mutum daya daga cikin ababen zargin da suka aikata wannan mummunar ta'asa.

A wani rahoton kuma, a kalla mutane takwas aka raunata yayin wani rikici da ya barke a tsakanin mabiya darikun addinin Musulunci biyu a kan jagorantar Sallah a babban Masallacin garin Okene da ke jihar Kogi.

Kafin wannan rikicin, da ma can akwai wata jikakkiya a tsakanin mabiya Tijjaniyya da Sunni a kan wanda zai gaji kujerar babban limamin Masallacin, Alhaji Musa Galadima, wanda ya mutu a cikin watan Afrilu na shekarar 2019.

Shaidar gani da ido ya ce rikicin ya samo asali ne bayan wani dan Izala mai suna Mallam Bello Hussaini ya kira limamin Masallacin, Sheikh Salihu, da mukaddashin liman yayin da ya shigo Masallacin.

Kalaman mabiyin Izalar sun fusata wani mabiyin Tijjaniyya mai suna Momoh Jimoh, wanda ya bukaci Malam Hussaini ya nemi afuwar babban Liman a kan cin fuskar da ya yi masa.

Shaidar ya sanar da 'TheNation' cewa lamarin ya haifar da hargitsi tare da yi wa Jimoh mugun duka tare da ji masa rauni a ka.

Faruwar hakan ta haifar da bawa hammata iska a tsakanin mabiya darikun guda biyu, lamarin da ya sa wasu Masallatan tserewa daga Masallacin.

An shafe kusan sa'a guda ana rikici kafin daga bisani 'yan sanda da sojoji su kwantar da tarzomar.

An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

Sai dai, kafin zuwan jami'an tsaron, a kalla mutane takwas ne su ka samu raunuka daban-daban yayin rikicin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel