Cacar baki ya kaure tsakanin dan gwamna da yan majalisa kan badakalar naira biliyan 4.3

Cacar baki ya kaure tsakanin dan gwamna da yan majalisa kan badakalar naira biliyan 4.3

Babajide, dan gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya caccaki majalisar dokokin jahar biyo bayan binciken da suka kaddamar kan wasu makudan kudade da suka gano gwamnati ta boye.

Sahara Reporters ta ruwaito majalisar ta bankado zambar kudi naira biliyan 4.3 ne da gwamnatin jahar ta taskance su a wani asusun sirri, ba asusun bai daya na jahar ba.

KU KARANTA: Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP

Sai dai dan gwamnan, Babajide, ya soki yan majalisar da yin maganganu marasa amfani game da kudade inda yace:

“A shekarar 2018 lamarin nan ya faru, kuma a bangaren zartarwa ta mika rahoton binciken kudi da ta yi ga majalisar, me yasa sai a yanzu suke tayar da maganan?”

Cacar baki ya kaure tsakanin dan gwamna da yan majalisa kan badakalar naira biliyan 4.3

Gwamna da Dansa Hoto: Orientaltimes
Source: UGC

Haka zalika ya zargi yan majalisar da tayar da maganan tare da siyasantar da ita saboda su cimma manufarsu ta gurgunta mahaifinsa yayin da zaben gwamnan jahar ke karatowa.

“Bana ji wannan farar dabara ce, wadannan bayanai ba’a a boye suke ba, an gudanar da kare kasafin kudi har sau biyu, an yi zaman sauraron korafe korafe a majalisar, amma babu wanda ya taba tayar da batun sai a yanzu?

“Shin ko shugaban kwamitin bacci yake yi a bakin aiki bai san aikinsa ba? Muna nan muna binciken abin da ya faru a 2018, a maimakon mu fara tambayar bangaren zartarwa mai suka shirya ma jahar bayan COVID19.

“Me zai faru shekaru masu zuwa idan gwamnatin tarayya ta daina samun kudaden shiga da za ta rabar ma jahohi, COVID-19 ta lalata hanyoyin samun kudin gwamnatoci, abin da ya wuce ya wuce, idan dai da gaske muke, dole ne mu mayar da hankalinmu zuwa gaba.

“Mu daina siyasantar da rayukan jama’anmu, a gaskiya wasa muke yi a yanzu.” Inji shi.

Babajide ya ce bayan an gano kudin a 2018, sai ya zama tamkar kari ne ga kasafin kudin gwamnati, don an kashe kashi 85 wajen biyan albashin ma’aikatan jahar.

Sai dai a hannu guda, shugaban kwamitin majalisar dake gudanar da binciken, dan majalisa Ademola Edamisan ya bayyana cewa zasu gudanar da aikinsu ba tare da bita da kulli ba.

Ya ce binciken su zai hada da tushen inda aka samu kudi, tare da kudin ruwan da ya tara tsawon shekaru 10.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel