Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 20 a Bauchin Yakubu

Yanzu-yanzu: An sallami masu Coronavirus 20 a Bauchin Yakubu

Gwamnatin jihar Bauchi ta sallami masu muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus (COVID-19) guda 20 dake cibiyar killacewanta.

Gwamnan jihar da kansa, Bala Mohammed, ya bayyana hakan a shafinsa na Twita ranar Litinin, 18 ga Mayu, 2020.

Ya ce da wannan sabon adadin na wadanda aka sallama, jihar ta samu nasarar jinya da sallamar mutane 89.

Bala Mohammed ya mika godiyarsa ga ma'aikatan asibitocin bisa jajircewars wajen yaki da annobar Korona.

Hakazalika ya yabawa kwamitin kar ta kwanan yaki da Koronan jihar tare da wasu masu ruwa da tsaki bisa taimakon suke badawa wajen yakin cutar.

Kawo ranar 1 ga Mayu, jimillan wadanda suka kamu da cutar a jihar 215, a cewar hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC.

Yace: "Ina farin cikin sanar da warkewa tare da sallamar karin masu cutar COVID19 20 daga cibiyoyin killacewarmu. Yanzu adadin wadanda muka sallama a jihar ya kai 89."

KU KARANTA: Coronavirus: Madagascar ta bukaci Najeriya ta biya kudin maganin da ta aiko

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 338 ne aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin 11:20 na daren Lahadi a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha.

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:10 na daren ranar Lahadi, 17 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 5959 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 1594 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 182.

A ranar Asabar ne ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da mutuwar karin mutane biyu da suka kamu da cutar korona.

Ma'aikatar ta sanar da haka ne a sanannen shafinta na tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel