Gambari: Gwamnonin Najeriya sun aika ma sabon shugaban ma’aikatan Villa muhimmin sako

Gambari: Gwamnonin Najeriya sun aika ma sabon shugaban ma’aikatan Villa muhimmin sako

Kafatanin gwamnonin Najeriya 36 sun yi alkawarin yin aiki kafada da kafada tare da sabon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Farfesa Ibrahim Agboola Gambari.

Gwamnonin sun bayyana haka ne cikin wata wasikar taya murna da suka aika masa wanda ta samu sa hannun shugaban kungiyar gwamnonin, gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi.

KU KARANTA: Bayanai sun bayyana game da abin da ya sabbaba sallamar Sule Hunkuyi daga PDP

Kungiyar ta ce akwai bukatan taimakekeniya tsakanin bangarorin biyu musamman saboda rashin tabbas da ake samu game da farashin danyen mai da kuma matsalar annobar Corona.

Kungiyar ta bayyana gamsuwarta da nadin Gambari musamman duba da matakan iliminsa, kwarewarsa, gogewarsa da kuma sanayyarsa a matakin Najeriya da kasa da kasa.

Gambari: Gwamnonin Najeriya sun aika ma sabon shugaban ma’aikatan Villa muhimmin sako
Gambari da Fayemi Hoto: Facebook
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito sanarwar kamar haka: “Muna farin ciki da cigaban da ka samu, kuma muna maka fatan alheri tare da shiriyar Ubangiji a wannan babban aiki mai cike da kalubale da aka rataya a wuyanka.

“Amma kamar yadda ka sani ne, akwai kalubale da wannan nadi, kuma aikin na bukatar biyayya, juriya, tsayar da hankali wuri guda, gaskiya da kuma taka tsantsan. A shirye mu ke yi aiki tare da kai don ciyar da kasarmu gaba.

“Musamman a yanzu da farashin mai ke kwan gaba kwan baya, ga kuma matsalar annobar Coronavirus.” Inji sanarwar.

A wani labarin kuma, bayanai sun fara bayyana game da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta jahar Kaduna ta dakatar da Sanata Othman Suleiman Hunkuyi tare da mutanensa guda shida.

Daily Trust ta ruwaito sakataren watsa labaru na jam’iyyar, Ibrahim Alberoh Catoh ne ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, 16 ga watan Mayu bayan wani zama da PDP ta yi a Kaduna.

A cewarsa PDP ta yi biyayya ga sashi na 57(3) na kundin tsarin mulkinta na 2017 wajen zartar da wannan hukunci a kan Suleiman Hunkuyi, tsohon Sanatan yankin Kaduna ta Arewa.

Majiyoyi daga cikin PDP sun bayyana matakin baya rasa nasaba da shigar da jam’iyyar kara da Hunkuyi yayi jim kadan bayan an kammala zaben shuwagabanni a matakin mazabu a Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel