TCN: SSAEAC su na neman yin yajin aiki saboda sallamar Shugabansu

TCN: SSAEAC su na neman yin yajin aiki saboda sallamar Shugabansu

Wasu manyan ma’aikatan wutan lantarki a Najeriya da ke karkashin kungiyar SSAEAC sun fara barazanar tafiya wani sabon yajin aiki saboda abin da ta kira saba doka.

‘Yan kungiyar SSAEAC sun bayyana tsige shugabansu watau Dr. Chris Okonkwo da aka yi a matsayin saba doka, don haka ta fara huro wutan shiga wani danyen yaji.

Jaridar The Nation ta ce bayan haka kungiyar ta zargi shugaban kamfanin TCN mai jan wuta a Najeriya da laifuffuka da su ka hada da cin amanar dokokin kwadago.

A ranar 24 ga watan Afrilun 2020 ne shugaban kamfanin TCN na kasa, Umar Mohammed ya sallami jagoran kungiyar SSAEAC watau Dr. Chris Okonkwo daga aiki.

TCN ta rubutawa Okonkwo wasika ta na mai cewa: “Bayan kusan shekaru shida a kamfanin TCN, ka sani cewa aikinka ya tsaya cak daga ranar 11 ga watan Yunin 2018”

A wasikar, kamfanin TCN ta bukaci Okonkwo ya daina zuwa ofis daga ranar 12 ga watan Yuni. A dalilin hakan, kungiyarsa ta SSAEAC ta ke ganin ba yi masa adalci ba.

KU KARANTA: Babu maganar shan wuta kyauta a Najeriya - Inji TCN

TCN: SSAEAC su na neman yin yajin aiki saboda sallamar Shugabansu
Shugaban TCN. Hoto daga: Energy Mix Report
Asali: UGC

Sakataren kungiyar na kasa, Abubakar Dubagari ya gargadi kamfanin TCN da ta yi maza ta janye wannan sallama da ta yi. Dubagari ya fitar da jawabi a madadin kungiyar.

A cewar kungiyar, za ta yi amfani da duk wata dama da ta ke da ita a doka wajen ganin an dawo da Okonkwo a kan mukaminsa. Hakan na nufin za ta iya tafiya yajin aiki.

Kungiyar ta ce Mohammed a matsayinsa na shugaban kamfanin TCN bai da hurumin da zai sallami Okonkwo. Ta ce wannan nauyi ya rataya ne kan ministan lantarki.

“Nadin mukaminsa ba kamar na sauran ma’aikatan TCN ba ne da za a iya yi wa mutum ritaya bayan ya kai shekara 60 ko kuma ya yi shekaru 35 ya na aiki.” Inji Dubagari.

“Kujerarsa ba ta da wa’adi, ba za a iya cewa aikinsa da TCN ya zo karshe a ranar 11 ga watan Yuni ba.” SSAEAC ta tunawa TCN cewa ka da ta saba tsarin da ake tafiya a kai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel