Harin ta’addanci: Bom ta tashi da wani gwamna da masu gadinsa a cikin mota

Harin ta’addanci: Bom ta tashi da wani gwamna da masu gadinsa a cikin mota

Wani gwamna a kasar Somaila. Ahmed Muse Nur tare da masu gadinsa sun rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar wani harin kunar bakin wake da aka kai musu a ranar Lahadi.

Kamfanin dillancin labarun AFP ta ruwaito lamarin ya faru ne a birnin Galkayo, yayin da Ahmed, wamnan lardin Mudug ta Arewa ta tsakiya ke cikin tafiya a ayarin motocinsa.

KU KARANTA: Korona: Sabbin mutane 338 sun karu a Najeriya, mutane 64 a Kano

Dan kunar bakin wake a cikin scooter ne ya buga ma ayarin motocin gwamnan, daga nan ya tashin bamabaman da yayi jidiga dasu, nan take gwamnan, direbansa da masu gadi suka mutu.

Wani shaidan gani da ido, Bile Mohamed ya bayyana harin kamar haka: “Kowa da kowa dake cikin motar ya mutu, tun daga gwamnan har da direbansa, hayaki ya turnuke ko ina, haka zalika wuta.”

Harin ta’addanci: Bom ta tashi da wani gwamna da masu gadinsa a cikin mota
Motocin gwamnan Hoto: Punch
Asali: Facebook

Tuni kungiyar ta’addanci ta mayakan Al-Shabbab ta dauki nauyin kai harin. A watan Maris da ta gabata ma Al-Shabaab ta kashe gwamnan Puntland a irin wannan yanayi.

A ranar Lahadin, kungiyar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa: “Mayakin mu wanda yayi shahada ya kashe gwamnan gwamnatin kafirci ta Mudug a Galkayo a yau.”

Birnin Galkayo na da nisanin kilomita 600 daga birnin Somalia, watau Mogadishu, an sha samun rikita rikita daga bangarorin yan ta’adda da kuma rikicin kabilanci a garin.

A shekarar 2011 aka fatattaki Al-Shabaab da kungiyar Al-Qaeda daga Mogadishu, amma har yanzu suna rike da yankuna da dama a Somalia, sun yi alwashin kifar da gwamnatin kasar.

A wani labarin kuma, gwamnan jahar Oyo a Najeriya, Seyi Makinde ya bayyana cewa sun garkame wani kamfani a jahar da aka samu ma’aikatanta su 30 dauke da cutar Coronavirus.

Gwamna Makinde ya bayyana haka ne a daren Lahadi, inda yace baya ga garkame kamfanin, zasu tsaftace ta ta hanyar yi mata feshin magani don kauce ma yaduwar cutar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel