Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle

Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle

Gwamnatin Kaduna ta sanar da sauyi a ranaku biyu a cikin sati da ake sassauta dokar kulle jihar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Muhammad Hafiz Bayero, manajan darektan kamfanin raya kasuwannin jihar Kaduna (KMDMC), gwamnatin ta ce za a sassauta dokar a ranakun 20 da 21 na watan Mayu.

Sanarwar ta ce mazauna jihar Kaduna za su iya fita zuwa makwabtan kasuwanni a ranakun domin sayen kayan abinci da sauran kayan amfani.

Sai dai, hakan na nufin ba za a bude kasuwannin jihar a ranar Asabar ba kamar yadda aka saba a baya.

A cewar sanarwar, ana bukatar duk wanda zai fita zuwa kasuwa ya saka takunkumin rufe fuska tare da gujewa cunkusshewa a wurin guda yayin sayayya a kasuwanni.

DUBA WANNAN: An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

KMDC ta shawarci jama'a su bawa hukuma hadin kai wajen biyayya ga matakan kare kai da dakile yaduwar cutar korona da gwamnati ta dauka.

Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle
Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle
Asali: Twitter

Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle
Gwamnatin Kaduna ta yi sauyi a ranakun sassauta dokar kulle
Asali: Twitter

Daga jihar Katsina mai makwabtaka da Kaduna, gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya bayar da umarnin sassauta dokar kulle jihar Katsina na tsawon mako guda.

Sakataren gwamnatin jihar Katsina (SSG), Mustapha Inuwa, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Asabar.

Ya bayyana cewa gwamnati ta yanke shawarar sassauta dokar ne bayan ganawarta da shugabannin addini da sauran masu ruwa da tsaki a jihar yayin taron da ta saba gudanarwa.

Inuwa ya bayyana cewa sassauta dokar kullen za ta fara aiki ne daga ranar Litinin, 18 ga watan Mayu, zuwa ranar Lahadi, 24 ga watan Mayu.

Ya ce za a sassauta dokar ne a cikin kananan hukumomin jihar, amma kuma dokar hana bulaguro zuwa wasu kananan hukumomin ta na nan daram.

Ya bayyana cewa gwamna Masari ya umarci sarkin Daura da na Katsina da sauran manyan masu rike da sarautar gargajiya a kan su tabbatar da cewa dagatai sun zauna a garuruwansu tare da jama'arsu yayin bukukuwan Sallah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel