Babu wanda ya kamu da korona a yayin da cutar ta kashe karin mutum 2 a Kano ranar Asabar

Babu wanda ya kamu da korona a yayin da cutar ta kashe karin mutum 2 a Kano ranar Asabar

- Babu wanda aka sanar da cewa ya kamu da kwayar cutar korona a Kano ranar Asabar

- Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanr da cewa an sallami masu jinyar korona biyu bayan an tabbatar da cewa sun warke sarai

- Annobar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a ranar Asabar

Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta sanar da mutuwar karin mutane biyu da suka kamu da cutar korona.

Ma'aikatar ta sanar da haka ne a sanannen shafinta na tuwita.

"Ya zuwa karfe 11:55 na daren ranar 16 ga watan Mayu, an samu karin mutane biyu da cutar korona ta kashe, yayin da aka sallami karin wasu mutanen biyu daga cibiyar killacewa.

"Jimillar mutanen da aka sallama ya zuwa yanzu sun kai 93, babu wanda ya kamu da cutar a yau, Asabar," a cewar sanarwar.

A cikin karin mutane 176 da hukumar NCDC ta sanar da cewa sun sake kamuwa da cutar korona a ranar Asabar, ba a samu wanda ya kamu da cutar a Kano ba ranar Asabar.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 176 a fadin Najeriya.

Babu wanda ya kamu da korona a yayin da cutar ta kashe karin mutum 2 a Kano ranar Asabar

Cibiyar killace masu cuttar korona a Kano
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11.56 na daren ranar Asabar, 16 ga watan Mayun na shekarar 2020.

DUBA WANNAN: Mayakan Boko Haram sun kai hari sansanin sojoji da motocin yaki 10, sun kashe dakaru 5

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutum 176 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

95-Lagos

31-Oyo

11-FCT

8-Niger

8-Borno

6-Jigawa

4-Kaduna

3-Anambra

2-Edo

2-Rivers

2-Nasarawa

2-Bauchi

1-Benue

1-Zamfara

Alkalluman da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar 16 ga watan Mayun 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu ta cutar ta korona a kasar 5,621.

An sallami mutum 1,472 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 176.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel