Yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga 9 a jihar Niger

Yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga 9 a jihar Niger

- A kalla 'yan bindiga tara ne suka rasa rayukansu sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin su da 'yan sanda tare da 'yan sa kai

- Rundunar 'yan sandan Operation Puff Adder da ke jihar Neja ce ta tunkari 'yan bindigar da suka gallabi jama'ar kauyukan Karaya Mahanga da Bakachi da ke karamar hukumar Rafi

- Biyu daga cikin 'yan bindigar sun nemi tserewa amma sai aka taresu tare da banka musu wuta ta yadda har ba a iya ganesu

'Yan bindiga tara ne suka rasa rayukansu sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin 'yan sanda da 'yan sa kai a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Al'amarin ya faru ne a kauyukan Karaya Mahanga da Bakachi da sa'o'in farko na ranar Asabar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa, 'yan bindigar sun yi artabu da 'yan sanda da kuma 'yan sa kai a kauyen Mekujeri da ke kusa da Kagara ta karamar ta karamar hukumar Rafi ta jihar.

Ya ce DPO din Kagara ya gaggauta tura rundunar Operation Puff Adder tare da wasu 'yan sa kai wadanda suka dinga ruwan wuta da 'yan bindigar da suka dade suna gallabar jama'ar Rafi da kewaye.

'Yan sanda sun yi wa 'yan bindiga 9 kisan kiyashi a jihar Niger

'Yan sanda sun yi wa 'yan bindiga 9 kisan kiyashi a jihar Niger. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: COVID-19: Masari ya dage dokar kulle a kananan hukumomi biyu

Ya ce, "Yan bindiga tara ne suka rasa rayukansu yayin da uku daga cikinsu suka tsere zuwa kauyen Mekujeri amma sai aka kama su tare da banka musu wuta har suka kurmushe.

"An samu Shanu da Tumaki 150 da suka sata bayan ruwan wutar da aka yi musu."

Shugaban karamar hukumar Rafi, Isma'ila Modibo, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust tattaunawar da aka yi da shi ta wayar tafi-da-gidanka. Ya shawarci mazauna yankin da kada su tsorata.

A wani labari na daban, gwamnatin jihar Katsina ta dage dokar kulle da ta saka a baya a kananan hukumomin Mani da Safana a jihar kamar yadda This Day ta ruwaito.

Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya amince da dage dokar zaman gidan nan take kamar yadda yake cikin sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustaha Inuwa ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel