Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi, Muhammad Bello, rasuwa

Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi, Muhammad Bello, rasuwa

Tsohon ministan ilimi, Alhaji Muhammad Bello Dogondaji, ya rasu yana da shekaru 84 a duniya. Ya rasu a ranar Juma'a a asibitin koyarwa na jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto bayan gajeruwar rashin lafiya.

Hassan Bello a madadin iyalan mamacin ne ya sa hannu a kan takardar sanarwar mutuwar.

Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi, Muhammad Bello, rasuwa

Allah ya yi wa tsohon ministan ilimi, Muhammad Bello, rasuwa. Hoto daga Jaridar Daily Trust
Source: Twitter

Kamar yadda majiyar ta tabbatar, marigayi Santurakin Sokoton ya fara fama da shanyewar barin jiki kuma an kwantar da shi a sashin kula na musamman.

Bayan sa'o'i shida da kwantar da shi a assibitin, sai yace ga garinku.

Muhammad Bello Dogondaji ya rasu ya bar mata, yara 17 da kuma jikoki.

Alhaji Bello ya yi rayuwa a matsayin malami kuma ya halarci jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria da kuma jami'ar Birmingham.

Ya yi ayyuka da dama a matakin jiha da tarayya har ya kai ga matakin ministan ilimi tsakanin watan Janairu na 1993 zuwa watan Janairu na 1994.

Takardar ta bayyana cewa tsohon ministan ilimin jinin sarautar jihar Sokoto ne,

Allah ya ji kansa, ya gafarta masa tare da yafe mas kura-kuransa.

KU KARANTA: Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje

A wani labari na daban, a ranar Juma'a ne ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce an samu sauki a jihar Kano tare da daidaituwa bayan hadin guiwar wakilan gwamnatin tarayya da kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano.

Ehanire ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya ce, "Daga cikin nasarorin da muka samu a jihar Kano shine karuwar yawan wadanda ake wa gwaji. Ana gwada a kalla mutum 350 a rana daya."

Ya ce gwamnatin jihar Kano na matukar kokari wajen bude sabbin cibiyoyin killacewa a jihar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce kwamitin yaki da cutar na jihar Kano zai horar da manema labarai a ranar Asabar, don tabbatar da 'yan jaridar na sako rahotanni a kan cutar yadda ya dace.

Ya ce horarwar za ta matukar taimakawa wajen wayar da kan 'yan jaridun a kan hanyoyin kariya daga cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel