Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Yakubu Bityong, ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Yakubu Bityong, ya rasu

- A daren Juma'a ne wurin karfe 11 na dare tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Yakubu Bityong ya rasu

- Bityong wanda ya taba kwamishina har sau uku, ya wakilci mazabar Kaura ta jihar Kaduna tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019

- Makusancinsa mai suna Umaru Spider ne ya tabbatar da rasuwarsa sakamakon ciwon huhu wanda ya tashi a jiya Juma'a da dare

Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Dr Yakubu Bityong, ya rasu.

Bityong ya wakilci mazabar Kaura a majalisar jihar tsakanin 2011 zuwa 2019. Ya rasu a daren Juma'a, 15 ga watan Mayun 2020 yana da shekaru 56.

Makusancin dan siyasan mai suna Yakubu Umaru Spider ne ya tabbatar da rasuwarsa ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna a ranar Asabar.

Umaru Spider, tsohon sakataren karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, ya ce an gano cewa Bityong na dauke da ciwon huhu ne a makonni biyu da suka gabata.

"Ya samu lafiya tare da ci gaba da rayuwarsa har zuwa jiya (Juma'a) yayin da ciwon ya sake buge shi.

"An kai shi babban asibitin Unguwan Boro wurin karfe 8:30 na dare, amma sai aka rasa likitan da zai duba shi. Bayan mintoci kadan da bugawar karfe 11 na dare sai yace ga garinku," yace.

Bityong ya rike mukamin kwamishinan ma'aikatun matasa da wasannin, kungoyin taimakon kai da kai da kuma ayyuka na musamman tsakanin 2003 da 2010.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, wanda ya ziyarci gidan mamacin ya ce ya tarar da iyalansa, manyan 'yan siyasa da sauran masu ta'aziyya.

Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Yakubu Bityong, ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon dan majalisar jihar Kaduna, Yakubu Bityong, ya rasu. Hoto daga The Cable
Source: UGC

DUBA WANNAN: COVID-19: Masari ya dage dokar kulle a kananan hukumomi biyu

A wani labari na daban, wata babbar kotu a jihar Zamfara ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani mutum da ya kashe mahaifiyarsa da yan uwansa mata biyu.

An gurfanar da Kamal Yusuf da wasu mutane biyu —Armayau Shehu da Caleb Humphrey a gaban kotu bisa zarginsu da aikata laifuka uku amma Humphrey ya mutu a gidan yari kafin a kammala sharia.

Laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa sun hada da hadin baki, fashi da makami da kisa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke zartar da hukuncin, babban alkalin jihar, Mai sharia Kulu Aliyu ta yanke wa Kamal Yusuf hukuncin kisa ta hanyar rayata yayin da shi kuma mutum na biyu da ake tuhuma, Armayau Shehu an wanke shi an kuma sake shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel