Kashe-kashen Katsina: FG ta dauka mataki mai tsauri

Kashe-kashen Katsina: FG ta dauka mataki mai tsauri

A yau Asabar 16 ga watan Mayun 2020, gwamnatin tarayya ta tura dakarunta don yaki da 'yan ta'addan da suka gallabi jihar Katsina.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa, Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da aka yi da shi a wani gidan rediyo a Katsina.

Masari ya ce dakarun sojin daga jihar da gwamnatin tarayya za a tura su sassan jihar ne don yaki da ta'addanci.

A yayin tattaunawa da gwamnan, ya jaddada cewa duk kalubalen tsaron ana kan shawo kansu, amma gwamnatin tarayya ce ke bada umarnin komai don ita ce mai rundunar sojin.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar ta samar da makamai da dukkan kayan aikin da sojin ke bukata don yaki da 'yan ta'addan.

Bincike ya nuna cewa, kananan hukumomi shida na jihar na cikin tashin hankali sakamakon harin da 'yan bindigar ke kai musu kullu yaumin.

Kananan hukumomin sun hada da: Bakori, Batsari, Safana, Sabuwa, Faskari da Kankara.

Masari ya sake bayyana cewa, za a sassauta dokar hana zirga-zirga a jihar a mako mai zuwa don samu a yi shagalin sallah mai zuwa.

Kashe-kashen Katsina: FG ta dauka mataki mai tsauri

Kashe-kashen Katsina: FG ta dauka mataki mai tsauri. Hoto daga jaridar HumAngle
Source: UGC

KU KARANTA: COVID-19: Gwamnatin tarayya ta bayyana halin da Kano ke ciki

A wani labari na daban, a ranar Juma'a ne ministan lafiya, Osagie Ehanire ya ce an samu sauki a jihar Kano tare da daidaituwa bayan hadin guiwar wakilan gwamnatin tarayya da kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano.

Ehanire ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa a Abuja.

Ya ce, "Daga cikin nasarorin da muka samu a jihar Kano shine karuwar yawan wadanda ake wa gwaji. Ana gwada a kalla mutum 350 a rana daya."

Ya ce gwamnatin jihar Kano na matukar kokari wajen bude sabbin cibiyoyin killacewa a jihar, jaridar Premium Times ta ruwaito.

Ya ce kwamitin yaki da cutar na jihar Kano zai horar da manema labarai a ranar Asabar, don tabbatar da 'yan jaridar na sako rahotanni a kan cutar yadda ya dace.

Ya ce horarwar za ta matukar taimakawa wajen wayar da kan 'yan jaridun a kan hanyoyin kariya daga cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel