Ma’aikatan jinya 15 sun mutu daga cutar korona

Ma’aikatan jinya 15 sun mutu daga cutar korona

Kungiyar ma'aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) a jiya Juma'a, ta bayyana cewa mambobi 15 ta rasa sakamakon annobar coronavirus a kasar nan.

Kamar yadda The Nation ta bayyana, a kalla ma'aikatan lafiya 20,000 da suka hada da likitoci da ma'aikatan jinya ne suka yi mu'amala da masu cutar. Ma'aikatan jinya 70 aka tabbatar da suna dauke da cutar yayin da aka killace 200 a halin yanzu.

A dukkan al'amarin, likitoci takwas da ma'aikatan jinya shida ne suka ransu sakamakon muguwar cutar.

Ma’aikatan jinya 15 sun mutu daga cutar korona

Ma’aikatan jinya 15 sun mutu daga cutar korona Hoto: WHO
Source: UGC

Shugaban NANNM, kwamared Abdulrafiu Adeniji ya sanar da hakan a yayin jawabi a taron ranar ma'aikatan jinya a Abuja.

Ya tabbatar da cewa rashin kayayyakin kariya da inshorar rayukan ma'aikatan jinyar na taka rawar gani wajen jefa su cikin wani hali.

Ya ce: "Sama da ma'aikata 2000 na lafiya a Najeriya ne suka yi mu'amala da masu cutar korona, yayin da 15 daga ciki suka ce ga garinku.

"Tsarin ma'aikatun lafiyar mu suna da manyan matsaloli a halin yanzu.

"Kamar yadda NANNM ta samu rahoton cewa ma'aikatan jinya 70 aka tabbatar da cewa suna dauke da cutar. Amma 200 ke killace. 600 an yi musu gwajin cutar yayin da ma'aikatan lafiyashida suka rasa rayukansu.

"Akwai karuwar yawan ma'aikatan jinya da ungozoma da ake cin zarafi, a boye musu labarin tafiye-tafiye da kuma ma'amala da masu cutar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Bijirewar majinyata tare da boye bayanai ne babbar matsalarmu - Kwamitin COVID-19

"Wannan lamarin na zama babban kalubale ga ma'aikatan lafiyar don ta nan suke kwasar kwayar cutar."

Ya kara da cewa, "Sama da kashi 25 na wadanda suka mutu sakamakon cutar coronavirus ma'aikatan lafiya ne."

Adeniyi ya kara da cewa gwamnatin tarayya ta samar da inshorar naira miliyan 20 zuwa 50 ga kowanne ma'aikacin lafiya a maimakon naira miliyan biyu da take son saka wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel