Kano: Bijirewar majinyata tare da boye bayanai ne babbar matsalarmu - Kwamitin COVID-19

Kano: Bijirewar majinyata tare da boye bayanai ne babbar matsalarmu - Kwamitin COVID-19

Jigon kwamitin yaki da COVID-19 a Kano, Dr. Tijjani Hussaini ya sanar da cewa babban kalubalen da suke fuskanta a jihar shine samun wadanda suka yi mu'amala da masu cutar amma suke kin zuwa gwaji.

Kamar yadda yace, wasu na musanta mu'amala da masu cutar duk da kuwa sun yi, tare da bada bayanan karya a kan lafiyarsu.

Bayan wannan bayanin a gaban kwamitin yaki da cutar korona na jihar, shugaban kwamitin fadar shugaban kasa, Dr. Sani Gwarzo ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kan kokarinsa na yaki da cutar.

Kano: Bijirewar majinyata tare da boye bayanai ne babbar matsalarmu - Gwarzo
Kano: Bijirewar majinyata tare da boye bayanai ne babbar matsalarmu - Gwarzo Hoto: The Cable
Asali: UGC

Dr. Gwarzo, wanda yace ya ji dadin yadda Ganduje ke ruwa da tsaki a kan al'amuran yaki da cutar a jihar, ya yi kira ga sauran gwamnoni da su yi koyi da halayyar gwamnan Kanon.

Gwarzo ya kara da mika godiyarsa ga Ganduje a kan yadda ya tabbatar da samuwar kayayyakin aiki don yaki da cutar.

Ya kara da cewa, baya ga wayar da kan jama'ar da Ganduje ya tabbatar ana yi a jihar, ya samar da takunkumin fuska kyauta ga mazauna jihar.

Ya kara da cewa, "Muna matukar farin ciki da yadda ake sallamar majinyata daga cibiyar killacewa a Kano. Wayar da kan jama'a da ake yi yasa suke kawo kansu gwaji. Wannan abun farin ciki ne kuma muna murna da yadda jihar ke shawo kan annobar."

Hakazalika, Shugaban kwamitin yaki da cutar korona na jihar Kano, Dr. Nasiru Gawuna ya tunatar da jama'a cewa kamuwa da cutar ba tikitin tafiya lahira bane.

Ya tunatar da jama'ar jihar amfanin kiyaye dukkan dokokin dakile yaduwar cutar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Akwai yuwuwar hauhawar yawan masu korona babu dadewa- Ganduje

A yayin jinjinawa jami'an tsaro kokarinsu na tabbatar da dokar hana zirga-zirga a jihar, Gawuna ya ce kwamitin yaki da cutar korona na jihar na kokari wajen wayar da kai.

"Muna tuntubar sarakunan gargajiya da malamai don sune suka fi kusa da jama'a. Suna taimaka wa wajen wayar da kan jama'a," Gawuna yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng