Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa

Gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya amince da nadin Lawal Maradun a matsayin sabon babban sakatarensa, PPS, inji rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN.

Sakataren watsa labaru na gwamnan, Jamilu Iliyasu ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a garun Gusai, inda yace haka nan gwamnan ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori uku.

KU KARANTA: Cikakken bayani game da aikin dakarun Soji a yankin Arewa maso gabas – DHQ

“Sabbin manyan sakatarorin sun hada da Alhaji Garba Ahmad, Alhaji Abubakar Jafar da kuma Alhaji Bala Umar.” Inji sanarwar.

Iliyasu ya kara da cewa Lawal Maradun ya kasance babban malamin a tsangayar ilimin jarida a kwalejin kimiyya da fasaha ta Abdu Gusa dake Talatan Mafara kafin wannan nadi.

“Alhaji Garba Ahmad kuma kafin wannan cigaba daya samu ya kasance shi ne daraktan kudi a hukumar kula da jin dadin alhazai ta jahar, shi kuma Alhaji Abubakar Jafar shi ne tsohon babban sakataren gwamna.

Gwamnan jahar Zamfara ya yi wasu muhimman nade nade guda 4 a gwamnatinsa
Gwamnan jahar Zamfara Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

“Sai kuma Bala Umar wanda ya taba zama jami’in kula da ofishin dake kula da alakar gwamnatin jahar Zamfara da gwamnatin tarayya a babban birnin tarayya Abuja.” Inji sanarwar.

A wani labari, gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da mutuwar manyan sakatarorinta guda biyu a cikin kwanaki biyu sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da suka yi fama da ita.

Manyan jami’an gwamnatin da suka mutu sun hada da Alhaji Yawale Dango, babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan jahar.

Sai kuma Alhaji Ahmed Sale, babbana sakatare a ma’aikatan gidaje da cigaban biranen jahar Zamfara. Sale ya rasu a ranar Talata, yayin da Dango ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

Shi ma a sakon ta’aziyya da ya fitar ta bakin hadiminsa a bangaren watsa labaru, Zailani Baffa, gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya yi addu’ar;

“Allah Ya shigar da su Aljanna, Ya baiwa iyalansu hakurin rashi.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel