Boko Haram: 'Yan ta'adda sun zubda iyalansu 72 a Borno bayan dakaru sun gallabe su

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun zubda iyalansu 72 a Borno bayan dakaru sun gallabe su

Sakamakon sabunta farmakin da dakarun sojin Najeriya suka yi a kan 'yan ta'addan yankin arewa maso gabas, mayakan Boko Haram da na ISWAP sun fara barin iyalansu tare da tserewa don tsira da rayukansu.

A yayin bayani ga manema labarai, shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche, ya bayyana cewa kusan iyalan 'yan ta'addan 72 wadanda suka hada da mata 33 da yara 39 aka bari a garin Ngala da ke karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

Kamar yadda yace, matan da kananan yaran na nan tare da rundunar sojin.

Boko Haram: 'Yan ta'adda sun zubda iyalansu 72 a Borno bayan dakaru sun gallabe su
Boko Haram: 'Yan ta'adda sun zubda iyalansu 72 a Borno bayan dakaru sun gallabe su Hoto: Daily Nigerian
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta wallafa, wasu mayakan ISWAP 11 sun yada makamai tare da mika kansu ga rundunar Operation Lafiya Dole a Adamawa.

Ya ce: "A ranar 12 ga watan Mayun 2020, mayakan ISWAP 11 ne suka mika kansu ga rundunar Operation Lafiya Dole ta jihar Adamawa.

"Tubabbun 'yan ta'addan suna nan hannun rundunar kafin a dauki mataki. Yawan mayakan da ke mika kai na bayyana irin zafin harin da dakarun sojin ke kai wa 'yan ta'addan.

"Akwai alamun da ke nuna cewa 'yan ta'addan suna son mika wuya. Daya daga ciki kuwa shine yadda suka bar iyalansu 72 a karamar hukumar Ngala ta jihar Borno.

"Dukkansu a halin yanzu suna hannun dakarun suna jiran mataki na gaba."

KU KARANTA KUMA: Bude masallatai da coci: FG ta yi wa gwamnatocin jihohi martani mai zafi

Ya kara da cewa, "Rundunar sojin Najeriya na amfani da wannan damar wajen kira ga iyaye, masu sarautar gargajiya da shugabannin addinai da su yi kira ga yaransu a kan gujewa shiga kungiyoyin ta'addanci saboda ba za su dade ba.

A halin yanzu 'yan ta'addan na nema mafaka."

A wani labarin na daban, mun ji cewa Farfesa Babagana Zulum na jihar Borno ya yi kira ga 'yan jihar da su dage wajen addu'a a kan Boko Haram da masu daukar nauyin su a sallolinsu na Tahajjud a kwanakin karshe na watan Ramadan.

Gwamna Zulum ya bukaci addu'ar ne a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis wacce mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau ya fitar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel