Kalli sabon faifan bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan yan Boko Haram a Borno

Kalli sabon faifan bidiyon yadda Sojoji ke ragargazan yan Boko Haram a Borno

Wani faifan bidiyo dake nuna yadda rundunar Sojin Najeriya ke ragargazan yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana a yanar Gizo.

Bidiyon ya nuna yadda wani dan Boko Haramun ke kokarin guduwa amma Sojojin suka masa ruwa harsasai har lahira sannan motar Igwan Sojin tabi ta kansa.

Jaridar Humangle ce ta saki bidiyon

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: Mutane 5 sun halaka yayinda sabon Rikici ya barke tsakanin kabilu biyu a jihar Adamawa

A bangare guda, Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana adadin sansanin zaman yan Boko Haram da ta tarwatsa cikin watanni ukun da suka gabata.

Hukumar ta ce yi nasarar tarwatsa matattarar 'yan Boko Haram 33 a cikin shekarar 2020.

Samamen da suka dinga kai wa ya dauka sa'o'i 1,700 inda suka halaka shugabannin kungiyar yan ta'addan.

Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan yada labarai da hulda da y na rundunar ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa sun kai samame har sau 889 ta jiragen yaki.

A yayin bayani ga shugaban rundunar sojin saman, Air Marshal Sadique Abubakar, a hedkwatar NAF da ke Maiduguri a ranar Laraba, Air Commodore Precious Amadi ya ce ayyukansu na daga cikin aikin rundunar Operation Rattle Snake na biyu da na uku da kuma Operation Decisive Edge.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel