Boko Haram ka iya amfani da annobar COVID-19 wajen kaddamar da hare-hare – UN ta gargadi Najeriya

Boko Haram ka iya amfani da annobar COVID-19 wajen kaddamar da hare-hare – UN ta gargadi Najeriya

Majalisar dinkin duniya ta ja kunnen cewa mayakan kungiyar yan ta'adda na Boko Haram na iya amfani da annobar COVID-19 wajen kai hari a sassan Najeriya.

A sabon rahoton tsaro da shawara na jami'an tsaron farin kaya da majalisar dinkin duniya ta bada, ta ce za a iya kiyaye hare-haren idan aka dauki matakin da ya kamata.

UNDSS ta ce bayanan sirri sun nuna cewa za a iya kai hare-haren ta hanyar amfani da abubuwa masu fashewa don tarwatsa wasu manyan ababen more rayuwa na kasa

Boko Haram ka iya amfani da annobar COVID-19 wajen kaddamar da hare-hare – UN ta gargadi Najeriya
Boko Haram ka iya amfani da annobar COVID-19 wajen kaddamar da hare-hare – UN ta gargadi Najeriya Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Rahoton ya ce, don kara rage karfin kokarin gwamnatin wajen yakar ta'addancin, kungiyar na iya amfani da al'amuran dakarun sojin da ke yankin arewa maso gabas don samun karbuwa.

"An gano cewa mun shiga wani kalubale na tsaro wanda ke kunshe da al'amura masu yawa. Sun hada da barazanar ta'addanci da kananan laifuka.

"Sun dade suna faruwa amma sai ga annobar Coronavirus ta bullo wacce za ta yi illa da gwamnati da yawan jama'a," rahoton da jaridar ThisDay ta samu ya bayyana.

"A yadda aka yi amfani da shi, ababen more rayuwa sune kayayyakin habbaka tattalin arziki da na tsaro. Sun shafi masana'antun man fetur, bankuna, Otal, shaguna da sauransu wadanda ke manyan birane kamar su Legas da Abuja," rahoton ya kara da cewa.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG

Don gujewa hare-haren, UNDSS ta bukaci hukumomin tsaron Najeriya da su gaggauta duba yanayin matakan tsaron Najeriya da gaggawa sannan a sauya su.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ja kunnen cewa akwai yuwuwar Boko Haram su fara kai hari a yayin da ake tsaka da annoba, amma ya bukaci 'yan Najeriya da su sa ido da kyau.

A gefe guda mun ji cewa rundunar sojin saman Najeriya ta yi nasarar tarwatsa matattarar 'yan Boko Haram 33 a cikin shekarar 2020.

Samamen da suka dinga kai wa ya dauka sa'o'i 1,700 inda suka halaka shugabannin kungiyar.

Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan yada labarai da hulda na rundunar ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa sun kai samame har sau 889 ta jiragen yaki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel