Bude masallatai da coci: FG ta yi wa gwamnatocin jihohi martani mai zafi

Bude masallatai da coci: FG ta yi wa gwamnatocin jihohi martani mai zafi

A ranar Alhamis ne gwamnatocin jihohi hudu na Arewa suka sanar da bude masallatai da cocinan su. Jihohin sun hada da Borno, Gombe, Adamawa da Zamfara.

Wannan babban al'amari ne da ya sassauta dokar kulle don dakile yaduwar annobar korona a kasar nan, jaridar The Nation ta ruwaito.

Gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin dadin ta a kan al'amarin ballantana da gwamnatocin jihohi ba su tuntubeta ba kafin sassauta dokar.

Baya ga haka, gwamnatin tarayya ta yarda da cewa har yanzu yaduwar kwayar cutar na a matakin farko ne.

Bude masallatai da coci: FG ta yi wa gwamnatocin jihohi martani mai zafi
Bude masallatai da coci: FG ta yi wa gwamnatocin jihohi martani mai zafi Hoto: The Cable
Asali: UGC

A daren jiya Alhamis ne NCDC ta tabbatar da cewa masu kwayar cutar coronavirus sun wuce 5,000 a kasar na da mace-mace kusan 200.

Kwamitin yaki da cutar korona ta fadar shugaban kasa ta yanke hukuncin jin ta bakin gwamnonin.

Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce: "Muna tattaunawa da kungiyar gwamnonin arewa. Mun san gwamnonin ba za su yi wani abu da zai jefa rayukan jama'arsu cikin garari ba tare da bata kokarin mu na makonni da suka wuce."

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya ya ce za a bude wuraren bauta ne kadai inda za a dinga saka takunkumin fuska, kiyaye dokar nesa-nesa da juna da kuma wanke hannu akai-akai.

Yahaya yace za a horar da wakilan wuraren bauta don tabbatar da sun bi dokoki tare da kiyaye su.

Ya ja kunnen jama'a da kada su kuskura su take wata doka, don lamarin zai sa ya mayar da dokar hana zirga-zirga. Ba zai jure saka lafiyar jama'a cikin garari ba.

Gwamnatin jihar Adamawa ta dage dokar hana taron addinai a take.

Sakataren yada labarai na gwamna Fintiri, Hunwashi Wononsikou ya ce: "Gwamna Ahmadu Fintiri ya sassauta dokar hana zuwa bauta bayan saka dokar da yayi don dakile yaduwar cutar coronavirus.

"Ya bada umarnin bude masallatai, coci da kasauwannin Shanu da ke rufe."

KU KARANTA KUMA: 'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG

Gwamnatin jihar Borno ta sanar da dage dokar hana zirga-zirga har sai yadda ta kama.

Gwamnatin ta tabbatar da cewa za a iya taron addinai amma a kiyaye dokoki tare da amfani da takunkumin fuska.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel