Minista Sadiya Umar Farouk ta bayyana tsarin da suke bi wajen ciyar da dalibai a gida

Minista Sadiya Umar Farouk ta bayyana tsarin da suke bi wajen ciyar da dalibai a gida

A ranar Alhamis ne gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin ciyar da dalibai daga gidajen iyayensu duk da cewa ba’a bude makarantu a Najeriya ba.

Punch ta ruwaito an kaddamar da ciyarwar ne a wata makarantar firamri dake garin Kuje a babban birnin tarayya Abuja, Central Science Primary School.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Gwamnan Kwara ya kori babban jami’in gwamnati saboda sakaci da aiki

Ministar kula da bala’o’i da walwalar jama’a, Sadiya Umar Farouk ce ta kaddamar da aikin, inda tace gwamnati na kashe daruruwan miliyoyi a duk rana don ciyar da daliban.

“Ba karamin aiki bane, kuma yana lakume manyan kudi saboda burinmu mu isar da abincin ga gidaje miliyan 3.1 a duk fadin Najeriya. Amma ba zan fada maka tabbataccen kudin da muke kashewa ba.” Inji ta.

Ministar ta ce tsarin mai suna National Home-Grown School Feeding Programme yana samun kudin kashewa ne daga gwamnatin tarayya, amma gwamnatocin jahohi ke gudanar da shi.

“Daga cikin matsalolin da annobar Coronavirus ta haifar akwai yunwa, shi yasa ma’aikatarmu ta yi ta kokarin samar da tsarin tallafa ma jama’a a wannan lokaci.” Inji shi.

Ministar ta ce ma’aikatar tare da hadin gwiwar gwamnatocin jahohi sun samar da tsarin kai abinci zuwa gidajen yaran da ke cin gajiyar ciyarwar a makarantu don cimma wannan manufa.

A hannu guda kuma, wani dake bin diddigin yadda ake gudanar da sabon ciyarwar, Valiant Samson Idowu-Alaba ya bayyana cewa ma’aikatar ta raba takardun shaida na ‘Voucher’.

Ana bayar da ‘Voucher’ ne ga iyayen da yaransu suke cin moriyar tsarin ciyarwar a makarantunsu.

Da wannan ‘Voucher’ ne iyayen zasu tafi wasu wurare da aka tanada don amsan kayan abincin.

Abincin sun hada da danyar shinkafa, wake, man gyada, man ja, kwai, tumatir da kuma gishiri. Ba wai gwamnati ke kai abincin da kan ta ba, iyayen ne suke karba a zababbun cibiyoyi.

Amma gwamnatin jahohi ne ke da hurumin zaben makarantun da zasu ci gajiyar tsarin bayan sun cika wasu sharudda, inji Valiant Samson Idowu-Alaba daga jahar Legas.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel