'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG

'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG

Daga yanzu, duk 'yan Najeriya da za su dawo daga kasashen ketare za su biya kudin killacesu da za a yi, kamar yadda sabbin tsarin suka bayyana.

A baya, wadanda za su iso daga kasashen ketaren ana bukatar su biya kudin jirginsu ne kadai yayin da gwamnati za ta dauki nauyin killace su da za a yi na makonni biyu.

'Yan Najeriya da suka dawo daga Dubai, Amurka da kuma Ingila duk suna otal a jihohin Legas da Abuja inda gwamnati ke daukar dawainiyar su.

'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG
'Yan Najeriya masu dawowa daga kasashen ketare za su biya kudin killacewa da ciyarwa - FG Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sabbin dokokin yanzu kuwa sun hana, kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

An tura sabbin dokokin zuwa ga ofisoshin jakadanci wadanda za su sanar da 'yan Najeriya masu niyyar dawowa gida.

Gwamnati ta ce ta saka kudin ne "saboda wasu matsaloli da suka kunno kai a kwamitin gudanarwa na COVID-19."

Alamu sun nuna cewa gwamnati ba za ta iya daukar dawainiyar masu dawowa gida ba. A kalla akwai 'yan Najeriya 4,000 da suka bayyana bukatar su ta dawowa gida Najeriya.

An gano cewa an fara sanar da masu dawowa kasar nan daga kasashen Thailand, Turkiyya da Kuwait.

A wasika mai kwanan wata 14 ga watan Mayu wacce ofishin jakadancin Najeriya ya fitar a Bangkok da ke kasar Turkiyya, ya ce ana bukatar N297,600 don killacewa tare da ciyar da masu son dawowa gida Najeriya.

Hakazalika, a ranar 13 ga watan Mayun 2020, 'yan Najeriya daga kasar Kuwait za su biya N297,600 baya ga kudin jirgin su na dawowa Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Romon damokaradiyya 10 da 'yan Najeriya za su mora bayan COVID-19 - Fadar shugaban kasa

Amma kuma wannan sabon lamarin ya sa 'yan Najeriyan suna ta zanga-zanga tare da guna-guni.

Wani maniyyaci da ya fadi ra'ayinsa a kan hakan, ya ce, "Ta yaya zamu iya biyan wannan zunzurutun kudin? Me yasa ba za su saka mu a otal mai arha ba wanda za mu iya biya?"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel