Katsina: 'Yan bindiga sun kai hari cikin dare, an rasa rai sannan sun raunata wasu
Mutum daya ya rasa ransa a yammacin Alhamis a garin Yankara da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina bayan harin da 'yan bindiga suka kai gidaje da dama a garin.
Wani mazaunin garin da ya zanta da SaharaReporters, ya ce kusan mutum takwas suka samu raunika kuma an garzaya dasu asibiti don samun taimakon likitoci.
Ya ce sama da Shanu 100 'yan bindigar suka yi awon gaba da su bayan harin.
Wannan na zuwa ne jim kadan bayan mazauna jihar sun nuna damuwarsu a kan yadda kashe-kashe da garkuwa da mutane ya ki ci balle cinyewa a jihar.
"Abin takaici ne idan muka tuna cewa shugaban kasa daga jihar mu yake amma ba mu da tsaro. Muna rayuwa cike da fargaba don ko bacci bamu iya yi.
"Ana kawo mana hari a kowanne lokaci, ko da rana kuwa," mazaunin yankin ya sanar.

Asali: UGC
KU KARANTA: Darus Salam: Sabuwar kungiyar ta'addanci da ta sauka a Arewa
A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sanar da isowar wata kungiyar 'yan ta'adda mai suna Darus Salam jiharsa, wacce ya kwatanta da kungiya mai tarin hadari.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa jihar Nasarawa na cikin matsanancin halin matsalar tsaro a cikin kwanakin nan.
Sabuwar kungiyar ta kware a garkuwa da manyan mutane na jihar kamar su mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar, sarakuna, sakatarorin gwamnati da sauransu.
A yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari, gwamnan ya danganta garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen da ake da kungiyar.
Kamar yadda yace, da farko kungiyar ta bar jihar amma da ta tashi dawowa sai ta iso da sabon karfinta inda ta sauka a wasu kananan hukumomi na jihar.
Gwamna Sule ya yi kira ga Shugaban Buhari da ya tura jami'an tsaro jihar don shawo kan lamarin kafin ya kai inda ba a tsammani kamar Boko Haram.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng