COVID-19: Mutum 193 sun karu a Najeriya, Kano, Jigawa da Yobe sun biyo bayan Legas

COVID-19: Mutum 193 sun karu a Najeriya, Kano, Jigawa da Yobe sun biyo bayan Legas

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa (NCDC) ta ce annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 193 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 12 na safiyar ranar Jumaa, 13 ga watan Mayun na shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa karin sabbin mutane 193 din sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka;

58-Lagos

46-Kano

35-Jigawa

12-Yobe

9-FCT

7-Ogun

DUBA WANNAN: Zamfara: Shugaban 'yan bindiga ya fitar da sautin murya, ya ja kunnen jama'a da kakkausar murya

5-Plateau

5-Gombe

4-Imo

3-Edo

3-Kwara

3-Borno

1-Bauchi

1-Nasarawa

1-Ondo

NCDC ta ce ya zuwa karfe 12:00 ranar Jumaa, 15 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 5,162 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar Covid-19 a fadin Najeriya.

An sallami mutane 1180 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 167.

A wani labarin, mun kawo muku cewa Rundunar Yan sanda ta jihar Sokoto ta kama mutum 155 daga karfe 8 na daren ranar Laraba zuwa karfe 6 na ranar Alhamis da suka saba dokar kulle da aka saka a jihar don dakile yaduwa annobar COVID-19.

Wannan na cikin wata sanarwa ce ta mai magana da yawun rundunar, Muhammad Sadiq, mai mukamin mataimakin superintendent na yan sanda ya fitar a ranar Alhamis a Sokoto kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mr Sadiq ya ce twagar hadin gwiwa ta jamian tsaro karkashin jagorancin kwamishinan Yan sandan jihar, Ibrahim Kaoje, daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 14 ga watan Mayu ta kama motoci da babura a kalla 63.

Ya ce, "An gudanar da ingattacen binciken a kan kamen da aka yi kamar yadda kwamishinan yan sanda ya bayar da umurni kafin a kai su kotu."

Ya bayyana cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin kama duk wani mutum ko kungiya ta aka samu da saba dokar ta hana fita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel