JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020

JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020

- Hukumar kula da jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta bayyana jihohi da aka fi samun magudi a jarabawar 2020

- Jihar Imo ce a kan gaba inda take da dalibai 27 da suka tafka magudi a jarabawar da aka yi ta watan Maris din wannan shekarar

- Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin ya sanar da cewa annobar korona ce ta tsayar da ala'amarin hukumar cak

Da dalibai 27 da suka yi magudin jarabawa a jihar Imo, jihar ta shugabanci jerin jihohi 31 da aka tafka magudin jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta 2020 da aka rubuta.

Jami'in hulda da jama'a na JAMB, Dr Fabian Benjamin ya sanar da jaridar The Nation cewa wasu dalibai 195 na nan a jerin sunayen wadanda suka yi magudi a jarabawar 2020.

Ya ce annobar Coronavirus ce ta datse al'amuran hukumar kula da jarabawar.

"An gurfanar da wasu daga cikin daliban yayin da wasu ake gab da gurfanar da su kafin annobar Coronavirus ta kawo tsaiko," yace.

Jihar Anambra ce ke biye da Imo a yawan daliban da suka yi satar jarabawar. Tana da dalibai 16 da aka kama da laifin. Jihohin Enugu, Kaduna da Kano ke biye da Enugu inda suke da dalibai goma sha biyar-biyar da suka tafka magudin.

JAMB: Jerin jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020
JAMB: Jerin jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa kwamishina rasuwa a Oyo

JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020
JAMB: Jihohi 5 da ke kan gaba wajen magudin jarabawar 2020. Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

A karshen jerin kuwa, akwai jihohin Adamawa, Sokoto, Gombe da Yobe inda dalibai dai-dai suka yi satar jarabawar. A babban birnin tarayya akwai dalibai uku yayin da Legas ke da dalibai tara.

Jihohi biyar ne da basu cikin jerin. Akwai jihohin Kebbi, Niger, Taraba, Bayelsa da Zamfara.

Dalibai 1,945,983 ne suka zauna jarabawar a watan Maris da ya wuce. Amma hukumar ta tabbatar da cewa yawan masu magudi a jarabawar ya ragu sosai a wannan shekarar.

Hakazalika, cibiyar jarabawar daya mai suna MS World ICT Institute of Information Technology da ke Kano aka hana yin jarabawar a 2020 sakamakon hada kai da take da dalibai wajen satar jarabawar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel