Aiki tukuru: Buhari ya zayyana wasu manyan ayyuka da zai gudanar bayan an shawo kan Coronavirus

Aiki tukuru: Buhari ya zayyana wasu manyan ayyuka da zai gudanar bayan an shawo kan Coronavirus

A yanzu haka kasashen duniya na cikin zullumin da halin da duniyar za ta shiga bayan an ga bayan annobar Coronavirus, watau COVID-19 duba da matsalolin da cutar ta haifar.

Annobar Coronavirus ta haifar da matsaloli bila adadin a kowanne bangaren rayuwa, musamman ma a kiwon lafiya, tsaro, harkar kudi da cinikayya, walwala, ayyuka da sauransu.

KU KARANTA: Masha Allah: Karamar yarinya yar shekara 6 ta warke daga cutar Coronavirus a Jigawa

Yan Najeriya na cikin rukunin mutanen dake da wannan zulumi, don haka gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fito da wasu sabbin tsare tsare.

Aiki tukuru: Buhari ya zayyana wasu manyan ayyuka da zai gudanar bayan an shawo kan Coronavirus

Buhari Hoto:Femi Adesina
Source: Facebook

Kakaakin shugaba Buhari, Femi Adesina ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, inda yace da wadannan tsare tsare ne gwamnati ke sa ran farfado da tattalin arziki inganta rayuwar yan kasa.

- Buhari ya kafa kwamitin da zai duba tasirin COVID-19 ga tattalin arzikin Najeriya a karkashin jagorancin ministan kudi

- Buhari ya kafa kwamitin da zai lalubo hanyoyin daidaita tattalin arzikin Najeriya a bayan COVID-19 a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa

- Buhari ya kafa kwamitin kar-ta-kwana da za ta saukaka hada hadar kayan amfanin gona a karkashin jagorancin ministan noma

- An samar da tsarin inganta cibiyoyin kiwon lafiya da asibitoci a duk jahohin Najeriya, tare da shirya su don kula da irin wannan matsala a gaba

- Za’a samar da tsare tsaren yin amfani da kayan gida wajen gudanar da bincike a kan magungunan cututtuka a fannin kiwon lafiya

- Samar da tsarin kula da kudade ta yadda CBN za ta cigaba da tallafa ma yan kasuwa da masu sana’o’i

Sauran sun hada da:

- Samar da babban shirin noma a kasar

- Gina manyan hanyoyi a yankunan karkara

- Gina gidaje da dama a kasar

- Sanya na’urar lantarki mai amfani da hasken rana a gidaje ta hanyar amfani da kayan aiki na gida

- Fadada tsarin bayar da tallafi na N-Power da ire irensu

- Sake nazari a kan kasafin kudin shekarar 2020

- Za’a fifita gudanar da manyan ayyuka masu muhimmanci fiye da sauran

- Karfafa dokokin da zasu yi yaki da rashawa da almubazzaranci

Yanzu abin da ya rage shi a yi fatan gwamnatin Buhari ta iya gudanar da wadannan kyawawan tsare tsare domin su fidda A’i daga rogo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel