Da duminsa: Lafiya ta samu, an sallamo Sarkin Daura daga asibiti

Da duminsa: Lafiya ta samu, an sallamo Sarkin Daura daga asibiti

An sallamo sarkin Daura, Farouk Umar Farouk daga asibiti kamar yadda kafar labarai ta TVC News ta ruwaito.

An kai sarkin asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Katsina bayan tsanantar rashin lafiyarsa.

Ana kai basaraken asibitin aka zarce da shi dakin kula na musamman (ICU) sakamakon halin da yake ciki.

Da duminsa: Lafiya ta samu, an sallamo Sarkin Daura daga asibiti

Da duminsa: Lafiya ta samu, an sallamo Sarkin Daura daga asibiti Hoto: TVC
Source: UGC

Bayan kwanaki kadan ne aka fitar da shi daga dakin sakamakon samun kanshi da aka fara yi.

An dai kai sarkin asibitin ne tun ranar 5 ga watan Mayu, bisa dalili na rashin lafiya da ba a bayyana irin ta ba.

A baya dai mun ji cewa mai martaba sarkin ya warke inda har ya karbi gaisuwa a harabar asibitin da aka kwantar da shi.

A bisa ga wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta, an nuna sarkin yana zaune a kan farar kujera ta roba yayin da mutane ke zuwa gabansa suna fadi suna gaisuwa tare da fadawa a tare da shi.

KU KARANTA KUMA: Masha Allah: Karamar yarinya yar shekara 6 ta warke daga cutar Coronavirus a Jigawa

Mai magana da yawun masarautar Dauram, Alhaji Usman Ibrahim ya tabbatar da sahihancin bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta.

Usman Ibrahim ya ce, "Tabbas wannan bidiyon da ke yawo, Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk ne, ya samu sauki sosai, huta wa ya ke yi yana jiran likitoci su sallame shi."

Ya kara da cewa, "Sarkin na godiya bisa adduoin da alumma suke masa kuma ya dauki wannan rashin lafiyar tasa a matsayin jarrabawa daga Allah."

A gefe daya, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya ce kwaskwarimar da aka yiwa kasafin kudin Najeriya na 2020 ba ta da wani muhimmanci wajen ceto tattalin arzikin kasar.

Atiku ya ce gyaran da aka yiwa kasafin kudin bana na rage Naira biliyan 71 daga cikinsa ba zai yi wani tasirin gaske ba wajen tsamo tattalin arzikin kasar nan daga halin da ya ke ciki a yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel