Obasanjo ya bayyana irin mawuyacin halin da 'yan Afrika za su shiga bayan COVI-19

Obasanjo ya bayyana irin mawuyacin halin da 'yan Afrika za su shiga bayan COVI-19

- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da tsohon firaministan kasar Ethiopia, Desalegn Boshe, sun nuna damuwa a kan nahiyar Afrika

- Sun ce kimanin mutane miliyan 80 za su fada cikin mummunan talauci idan ba a dauki matakan gaggawa ba

- Alkaluma daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun nuna akwai fiye da mutane 72,000 da aka tabbatar da cewa annobar korona ta harbesu

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, da takwaransa, tsohon firaministan kasar Ethiopia, Desalegn Boshe, sun yi kira a kan a mayar da hankali bunkasa harkokin noma da raya karkara a nahiyar Afrika.

Sun yi gargadin cewa nahiyar Afrika za ta iya kasancewa bangaren da annobar korona za ta fi yi wa illa a duniya, musamman tattalin arzikin nahiyar.

Sun yi kiyasin cewa a kalla 'yan Afrika mutum miliyan 80 za su fada cikin mummunan talauci sakamakon tsayar da al'amuran noma da kasuwanci da annobar korona ta yi.

Shugabannin biyu sun bayyana hakan ne ranar Alhamis a cikin wata takarda da suka hada gwuiwa wajen wallafata a shafin bunkasa harkar noma na kasa da kasa.

A cikin takardar, shugabannin sun gargadi kasashen nahiyar Afrika a kan yin burus da talakawan da ke rayuwa a karkara da kauyuka.

Obasanjo ya bayyana irin mawuyacin halin da 'yan Afrika za su shiga bayan COVI-19

Obasanjo
Source: Twitter

"A yayin da Afrika ta kubuta daga annobar korona, nahiyar kan iya fuskantar babban kalubalen tattalin arziki.

"Kimanin mutane miliyan 80 za su fada cikin mummunan talauci idan ba a dauki matakan gaggawa ba. Tsayawar harokin noma za ta iya jefa 'yan Afrika da dama cikin yunwa.

DUBA WANNAN: Tsare matashi a kan tsohon layin wayar diyar Buhari: Kotu ta ci tarar DSS miliyan N10

"Mutanen karkara, wadanda yawancinsu sun dogara ne da kananan sana'o'i, za su fi shan wahala da fuskantar matsin tattalin arziki.

"Ya na da matukar muhimmanci ga kasashe su mayar da hankali wajen bijiro da tsare - tsare da aiyukan da za su taimaki jama'ar da ke zaune a karkara.

"Kimanin kaso 65 na mutanen Afrika ba su da wani aiki da ya wuce noma, sannan noma ya kunshi kaso 75 na hadar - hadar cinikayya a kasuwannin Afrika.

"Za a iya amfani da noma wajen yaki da talauci tare da tsamo jama'a daga matsin tattalin arziki da annobar korona ta haifar," a cewar takardar.

Alkaluma daga hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun nuna akwai fiye da mutane 72,000 da aka tabbatar da cewa annobar korona ta harbesu.

Kazalika, alkaluman sun nuna cewa akwai fiye da mutane 25,000 da su ka warke daga cutar korona, yayin da annobar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 24,00 ya zuwa karfe 10:30 na safiyar ranar Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel