Abokai sun shatawa sabon Shugaban ma’aikatar fadar Shugaban kasa layin aikinsa

Abokai sun shatawa sabon Shugaban ma’aikatar fadar Shugaban kasa layin aikinsa

Abokai da manyan na-kusa da Farfesa Ibrahim Gambari, wanda aka nada a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, sun soma shirya masa aikin da ke kansa.

Masana da-dama sun fito su na cewa Ibrahim Gambari zai kawo gyara a fadar shugaban kasa da ma tafiyar gwamnatin Muhammadu Buhari saboda ilminsa da ma kwarewa a bakin-aiki.

1. Kasar waje

Daga cikin bangaren da ake sa ran Ibrahim Gambari zai taimakawa gwamnatin Najeriya shi ne gyara alakarsa da kasashen Duniya. Gambari ya na da mutane a ketare saboda aikin da ya yi a majalisar dinkin Duniya.

2. Tattalin arziki

Dr. Abubakar Umar Kari na Jami’ar Abuja ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa Ibrahim Gambari zai taimaki gwamnatin Najeriya wajen babbako da tattalin arzikin ta. Hadimin ya san manyan hukumomin da ake ji da su.

KU KARANTA: Yadda Buhari ya ba kowa mamaki wajen zaben Hadimin fadar Shugaban kasa

3. Rigimar ASUU da Gwamnati

Rahoton da jaridar ta fitar ya nuna sabon hadimin shugaban kasar ya taba karantarwa a jami’ar ABU Zariya. Farfesa Umaru Pate na BUK ya na ganin Ibrahim Gambari zai warware matsalar gwamnati da malaman jami’a.

4. Kawo gyara a salon mulki

Wani malami a jami’ar LASU, Farfesa Sylvester Odion, ya na da ra’ayin cewa zuwan Gambari zai canza yadda abubuwa su ke tafiya a fadar shugaban kasa. Ana kuma sa ran hadimin ya kawo sauyi a mulkin shugaba Buhari.

5. Raba nauye-nauye

Gambari zai koyi darasi daga Abba Kyari wanda ya rasu a kan kujerar. Tope Fasua ya ba Gambari shawarar ya rika raba ayyuka ga masana, ka da ya ce shi kadai ne zai rike komai a gwamnati ko ya rika ci wa shugaban kasa albasa.

6. Sulhu

Wani wuri da ake ganin Najeriya za ta ribatu da Ibrahim Gambari shi ne kokarinsa na iya yin sulhu da shiga yarjejeniya a matsayinsa na kwararre kuma malami a wannan fanni. Kuma bai da alaka da wata jam’iyyar siyasa a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel