Korona: Mutane 184 sun karu a Najeriya, Jigawa, Bauchi da Katsina sun biyo bayan Legas

Korona: Mutane 184 sun karu a Najeriya, Jigawa, Bauchi da Katsina sun biyo bayan Legas

Hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa a kasa (NCDC) ta sanar da cewa karin sabbin mutane 184 ne aka tabbatar da cewa sun sake kamuwa da kwayar cutar covid-19 a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar da misalin karfe 11:29 na daren ranar Laraba a shafinta na tuwita, ta fitar da jerin jihohi da jimillar ma su dauke da kwayar cutar a kowacce jiha kamar haka;

51-Lagos

23-Jigawa

16-Bauchi

16-Katsina

14-Kano

10-FCT

10-Rivers

9-Kwara

5-Delta

5-Kaduna

4-Sokoto

4-Oyo

3-Kebbi

3-Nasarawa

3-Osun

2-Ondo

1-Ebonyi

1-Edo

1-Enugu

1-Anambra

1-Plateau

1-Niger

NCDC ta ce ya zuwa karfe 11:29 na daren ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, akwai jimillar mutane 4971 da aka tabbatar da cewa suna dauke da kwayar cutar covid-19 a Najeriya.

An sallami mutane 1070 bayan an tabbatar da samun saukinsu, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 164.

DUBA WANNAN: An bude Masallatan kasar Iran albarkacin daren Lailatul Qadri

Daga cikin mutanen da aka sanar da cewa sun warke daga cutar korona a ranar Laraba akwai wata tsohuwa mai shekaru 98 da haihuwa wacce aka sallama daga cibiyar killace masu dauke da cutar a Legas.

Babajide Sanwo Olu, gwamnan jihar Legas ne ya sanar da hakan ta shafin Twitter a daren ranar Laraba.

Tana daya daga cikin mutane 26 da aka sallama a jihar ta Legas a ranar Laraba bayan an musu gwaji kuma sakamakon ya nuna sun warke.

Sakon da gwamnan ya wallafa a Twitter ya ce, "Yau, mun sallami wata tsohuwa mai shekaru 98, ita ce mai jinya mafi yawan shekaru da muka taba samu a nan jihar Legas.

"An sallameta tare da wasu majinyata 25; 13 maza, da 12 mata bayan gwajin da aka yi musu ya nuna sun warke daga cutar ta COVID19, hakan ya kawo jimillar wadanda suka warke zuwa 528."

Sanwo Olu ya kuma mika godiyarsa ga ma'aikatan lafiya da sauran ma'aikatan da ke kan gaba wurin yaki da annobar a jihar.

Ya kuma yi kira da mutanen jihar su cigaba da kiyayye sharrudan da hukuma ta saka domin kare kansu daga mummunar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel