Majalisar zartarwa ta ware N47bn don inganta lantarki a yankin Arewa maso gabas

Majalisar zartarwa ta ware N47bn don inganta lantarki a yankin Arewa maso gabas

Majalisar zartarwa a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da kashe N47bn don samar da karin wutar lantarki megawatt 40 a Najeriya.

Daily Trust ta ruwaito Ministan lantarki, Mamman Saleh ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa a ranar Laraba, inda yace za’a kwashi wutar ne daga jahar Taraba.

KU KARANTA: Wasu dabi’u na Ibrahim Gambari da suka burge Buhari har ya nada shi shugaban ma’aikatan Villa

Sale yace za’a samu 40 MW din daga madatsar ruwa ta Kashimbila jahar Taraba, sai a antaya ta jahohin Taraba, Benuwe da sauran jahohin yankin Arewa maso gabas don inganta wutansu.

Saboda haka Minista Mamman Saleh yace idan har Najeriya bata kwashe wannan wuta ba, za ta yi asarar kimanin dala miliyan 9 a shekara guda.

“Majalisar ta amince da bukatar ma’aikatan lantarki na bayar da kwangilar N47,235,303,821.90 don samar da kayan aiki domin kwashe lantarkin 40 MW daga Kashimbila tare da amfani da shi, ta hanyar Takum, Wukari da Yandev.” Inji shi.

Majalisar zartarwa ta ware N47bn don inganta lantarki a yankin Arewa maso gabas

Majalisar zartarwa Hoto: Buhari Sallau
Source: Facebook

Haka zalika ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa majalisar ta amince a kashe N683m don sayen motocin sufuri 19 ga hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, NPA.

“Wannan ne karo na farko da NPA za ta sayi motoci a cikin shekaru hudu, hakan ta sa majalisar ta amince da bukatar, motoci ne na aiki, ba wai na shuwagabannin hukumar ba, dukkansu Toyota ne.” Inji shi.

A wani labari kuma, Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon, EFCC, reshen jahar Sakkwato ta kama yan kasar China da laifin yi ma shugaban tayin cin hanci.

EFCC ta bayyana haka ne a shafinta na Facebook a ranar Talata, inda tace Meng Wei Kun da Xu Koi sun yi ma shugaban EFCC na reshen Sakkwato tayin cin hancin naira miliyan 100.

Sun fara yi ma shugaba Abdullahi Lawal tayin cin hancin N50,000,000 don ya dakatar da binciken da yake yi game da kamfanin China Zhonghao Nig Ltd bisa wasu ayyuka da take yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel