Satar Shanu: Ana neman kansila ruwa a jallo

Satar Shanu: Ana neman kansila ruwa a jallo

- Gwamnatin jihar Adamawa, karkashin jagorancin Gwamna Ahmadu Fintiri ta sanar da neman wani kansila da take ido rufe

- Kamar yadda gwamnatin ta sanar, tana neman Makana Enan Ngari da ke wakiltar gundumar Vulpi ta karamar hukumar Numan

- Ana zarginsa da sa hannu a satar wasu Shanu a daidai lokacin da karamar hukumar Numan da Demsa suka samu sauki lamarin

A ranar Laraba, 13 ga watan Mayun 2020, gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da cewa tana neman wani kansila ido rufe sakamakon zargin sa da ake da satar Shanu.

Kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa, gwamnatin ta sanar da sunan kansilan da Makana Enan Ngari. Yana wakiltar gundunar Vulpi ce da ke karamar hukumar Numan kuma ana zargin sa da hannu a satar Shanu.

Humwashi Wonosikou, sakataren yada labarai na Gwamna Ahmadu Fintiri, ya ce kansilan ya yi laifin ne a daidai lokacin da yankin Numan din suka fara samun saukin satar Shanun.

A yayin kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu, takardar ta ce gwamnati za ta dauka mataki mai tsauri a kan duk wanda ta kama da wannan laifin, komai kuwa matsayin sa.

Satar Shanu: Ana neman kansila ruwa a jallo
Satar Shanu: Ana neman kansila ruwa a jallo. Hoto daga NPR
Asali: Getty Images

DUBA WANNAN: Mutum 42,000 ne suka yi hijira daga jihohi 3 na yankin arewacin Najeriya - UNHCR

"Gwamnatin da ta san abinda take yi ba za ta kalmashe kafa tana kallon masu laifi suna tarwatsa zaman lafiyar da ta gina ba," takardar tace.

Numan da karamar hukumar Demsa ta jihar Adamawa sun sha fama da satar Shanu a kwanakin baya.

Lamarin ya yi sauki tun bayan zuwan gwamnatin Ahmadu Fintiri a shekarar da ta gabata. An samu daidaituwa da zaman lafiya a bayyane.

A wani labari na daban, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar da aka kwantar a asibitin kwararru na gwamnatin tarayya da ke Katsina tun ranar 5 ga watan Mayu sakamakon rashin lafiya da ba a bayyana irin ta ba ya warke inda har ya karbi gaisuwa a harabar asibitin.

Wani bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna sarkin yana zaune a kan farar kujera ta roba yayin da mutane ke zuwa gabansa suna fadi suna gaisuwa tare da fadawa a tare da shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel