Yanzu-yanzu: Bauchi ta sallami masu Coronavirus 17, 2 sun mutu

Yanzu-yanzu: Bauchi ta sallami masu Coronavirus 17, 2 sun mutu

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da sallamar mutane 17 masu fama da cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus bayan sun warke wassai. Hakazalika mutuwar karin mutane biyu.

A cewar Daily Trust, wannan na kunshe cikin jawabin kwamitin yakin cutar COVID-19 na Bauchi karkashin ma'aikatar lafiyan jihar ta saki ranar Laraba, 13 ga Mayu, 2020.

Jawabi yayi bayyana cewa da sallamar sabbin mutane 17, adadin masu cutar Korona da gwamnatin Bauchi tayi jinya kuma ta sallama ya kai 23.

Kawo yanzu, adadin wadanda suka kamu da cutar a jihar Bauchi ya kai 190 bayan sanarwan hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC.

Yanzu-yanzu: Bauchi ta sallami masu Coronavirus 17, 2 sun mutu
Yanzu-yanzu: Bauchi ta sallami masu Coronavirus 17, 2 sun mutu
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta kama yan China 2 da laifin baiwa shugaban EFCC cin hancin N100m

A bangare guda, A ranar Talata gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta tura wakilanta na ma'aikatar lafiya zuwa Azare da ke jihar Bauchi, Katsina da Jigawa sakamakon hauhawar yawan mace-macen da ke aukuwa wadanda ake danganta wa da cutar coronavirus.

Ministan lafiya, Dr. Osagie Ehanire, ya sanar da hakan a garin Abuja yayin tattaunawa da kwamitin fadar shugaban kasar na yaki da annobar COVID-19.

"Wakilai daga ma'aikatar lafiya ta tarayya sun isa jihar Bauchi don binciken hadin guiwa tare da gwamnatin jihar a kan mace-macen da ke aukuwa a Azare.

"Wasu wakilan sun isa jihar Katsina da Jigawa don bincika abubuwan da jihohi ke bukata don dakile yaduwar annobar. Akwai bukatar dakina gwaji wadanda rashinsu ke kawo koma baya a fannin gwajin kwayar cutar.

"Sauran yankunan da ke fama da barkewar cutar duk za a mika musu tallafin da suke bukata."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel