Tsohon kwamishinan Kano ya ba da labarin wahalar da ya sha yayin fama da cutar korona

Tsohon kwamishinan Kano ya ba da labarin wahalar da ya sha yayin fama da cutar korona

Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Mu'az Magaji, ya samu fitowa daga dakin bayar da kulawa ta musamman yayin da yake ci gaba da samun sauki bayan kamuwa da cutar korona.

A baya mun kawo rahoton yadda aka killace Injiya Magaji a daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar korona a jihar Kano.

Cutar korona ta harbi tsohon kwamishinan ne dai bayan kwanaki kadan da aka yi ta cece-kuce kan magana mai harshen damo da ya yi bayan mutuwar tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Babu shakka ana zargin Injiya Magaji ya wallafa wasu kalamai marasa dadi a kan shafinsa na dandalin sada zumunta dangane da mutuwar Abba Kyari, lamarin da ya musanta da cewa an yi masa mummunar fahimta.

Wannan lamari da ya wakana tun a watan Afrilun da ya gabata, ya sanya gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, bai yi wata-wata ba wajen tube kwamishinan daga mukaminsa.

A ranar Laraba, Injiya Magaji ya ba da labarin irin bakar wahala da ya sha yayin fama da cutar korona a daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar da ke Kanon Dabo.

Ya ce ko makiyinsa ba ya yi wa fatan ya kamu da wannan cuta da kawo yanzu masu ta-cewa a kanta suka kaddamar ba a samu riga-kafinta ba.

Tsohon kwamishinan ayyuka na Kano; Mu'az Magaji
Tsohon kwamishinan ayyuka na Kano; Mu'az Magaji
Asali: Facebook

Labarin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, tsohon kwamishinan ya yi magana a kan wani bangare na wahala mai tsananin gaske da cutar ta jefa shi ciki.

Ya bayyana irin addaba ta ciwon jiki mai radadi gami da rashin bacci da ya rika fuskanta yayin da ya ke dakin kulawa ta musamman da ake kira ICU (Intensive Care Unit).

KARANTA KUMA: Dattijon da ya rubuta Alqur’ani gaba daya da hannunsa ya rasu a Maiduguri

Yayin da har kawo yanzu ba a tabbatar da wani ingantaccen magani ba, tsohon kwamishinan ya ce waraka ce kawai ta zo masa daga Allah, sai dai ya yi riko da sababi wajen shan tsumin gargajiya, da sauran magunguna na al'ada gami da motsa jiki a kan kari.

Da ya ke jaddada girman cutar, ya ce sam babu siyasa game da lamarin kwayoyin korona domin kuwa cutar gaskiya ce sabanin yadda wasu ke ikirari da nuna rashin yarda.

Ya yaba da kwazon gwamnatin Kano da kuma tarrayya a bisa fadi-tashin da suke yi na kawo karshen wannan hatsabibiyar cuta.

Daga karshe ya kuma mika sakon godiya na addu'o'i da aka kwarara masa gami da jaje da aka rika yi masa ta hanyar kiraye-kirayen wayar salula da sakonni da aka rika aiko masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel