Ba zan iya auran mutum irin Dangote ba – Jarumar fim
- Oyinkasola Emmanuel ta yi bayanin irin namijin da take fatan kare rayuwarta da shi
- Kamar yadda jarumar ta bayyana, za ta so mutum mai tsoron Ubangiji wanda zai bata lokacinsa
- Emmanuel ta ce ba za ta iya auran mutum kamar Dangote ba duk kuwa da kudinsa
Jarumar fina-finan yarbawa da ta tashi a kasar waje, Oyinkasola Emmanuel ta yi magana a kan irin namjini da za ta so kare rayuwarta da shi. A take kuwa ta soke hamshakin mai kudi, Aliko Dangote daga cikin irin mazan da take so.
A wata wallafa da jarumar tayi a Instagram, Emmanuel wacce ta bayyana cewa ita gajera ce, za ta so auran dogon namiji.
Ta sake jaddada tsoron Allah da mutunci a cikin abubuwan da za ta so mijinta ya mallaka.
Ta ce, "Zan so auren mai tsoron Ubangiji wanda ya san yadda zai kula da mace. Dole ne ya kasance mai mutunci. Ba zan so namiji da zai iya komawa Mike Tyson ko Anthony Joshua ba bayan aure.
"Ban damu da tarin dukiya ba amma ina son namiji mai tsawo tunda ni gajera ce. Ba zan so haihuwar wadanni ba."
Ta bayyana cewa za ta so auren namiji mai rufin asiri amma ba za ta lamunci rashin zamansa a tare da ita ba.
Ta kara da bayyana cewa ba za ta iya auren Dangote ba saboda bashi da lokacin ta kuma babu kudin da zai iya janye hankalinta daga bukatar mijinta.
Ta kuma ce Dangote mutum ne da ba zai samu lokacin ta ba, kuma ba kowacce matsala bace kudi ke iya shawo kai ba.
KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun kama Edwin Congo da zargin dillacin hodar iblis a Sifen
Kamar yadda tace, "Ban ce bana son kudi ba. Zan iya auran mutum kuma in zauna komai kankantar arzikinsa matukar zai iya kula da bukatu na. Koda ba shi da miliyoyi, zan zauna da shi lafiya matukar da kula."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng