Coronavirus: Sanatocin Najeriya sun saba dokar ba da tazara a zaman majalisa

Coronavirus: Sanatocin Najeriya sun saba dokar ba da tazara a zaman majalisa

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya soki yadda wasu daga cikin sanatoci suka saba dokar ba da tazara yayin zaman majalisar da aka gudanar a yau Talata.

Shugaban majalisar ya fusata da wasu daga cikin abokanan aikinsa da suka saba wa dokokin da muhukuntan lafiya suka shar'anta da manufar dakile yaduwar cutar korona.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sanata Lawan ya bayyana rashin jin dadi a kan yadda wasu daga cikin sanatoci suka saba dokar ba da tazara yayin zaman majalisa da aka gudanar a ranar Talata, 12 ga watan Mayu.

Sanatan mai wakilcin shiyyar Yobe ta Arewa, ya lura da saba wa dokar ba da tazarar ne a yayin da yake karanto sakamakon zaman majalisar na Talatar makon da ya gabata.

Ya ce: "Ya ku abokanan aiki, a matsayinmu na shugabanni kuma masu shar'anta doka, mu taimakawa kawunanmu wajen tabbatar da yi wa dokar ba da tazara da'a."

"Na lura da yawan sanatoci sun saba dokar ba da tazara musamman wadanda ke zaune a kujerun baya."

"Don Allah, mu kasance mun zama madubin dubawa ga al'umma wajen tabbatar da kiyaye dokar ba da tazara da ake bukata a tsakanin kujerun da muke zazzaune."

'Yan mintina kada, shugaban majalisar ya sake maimaita gargadin da ya yi a baya, inda ya bayyana cewa, Sanata Uche Ekwunife ta jam'iyyar PDP mai wakilcin shiyyar Anambra ta Tsakiya, ta yi kusanci sosai da mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ovie Omo-Agege.

Shuagban majalisar dattawa; Sanata Ahmed Lawan; Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila a fadar shugaban kasa
Shuagban majalisar dattawa; Sanata Ahmed Lawan; Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila a fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

Sanata Lawan ya lura da yadda Sanata Uche ta zauna ba tare da bayar da tazara ba a tsakaninta da mataimakinsa, Sanata Agege na jam'iyyar APC mai wakilcin shiyyar Delta ta Tsakiya.

Shugaban majalisar ya kuma umarci sanatocin da su kasance sanye da takunkumin rufe fuska a duk sa'ilin da su ka bukaci yin magana.

Makonni biyu da suka gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sassauta dokar kulle wadda ya shimfida a jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja, a sanadiyar yadda cutar korona ke ci gaba da yaduwa a kasar.

KARANTA KUMA: Shekau ya na neman Allah ya kare shi daga sojojin Najeriya

Sai dai bayan ya sassauta dokar, shugaba Buhari ya kuma ba da umarnin a zage dantse wajen ba da tazara da kuma sanya takunkumin rufe fuska a yunkurin dalile yaduwar cutar.

Yayin da sannu a hankali an fara dawo wa al'amuran yau da kullum, shugaban kasar ya kuma sanya haramci a kan yin zirga-zirga a tsakanin jihohin kasar, illa iyaka ma'aikata na musamman da dole ake bukata da kuma kayan abinci.

Haka zalika mun ji cewa, kwamitin lura da cutar korona a Najeriya sun bayyana damuwa kan yadda 'yan kasar ba sa kiyaye dokar ba da tazara, inda suka yi barazanar shawartar shugaban kasa a kan sake shimfida wata sabuwar dokar kullen muddin ba a gyara ba.

A halin yanzu dai alkaluman Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC, sun nuna cewa, an samu mutum 4641 da cutar korona ta harba a fadin kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel