COVID-19: Mu na ji mu na gani ciwon hanji ya kashe Kaninmu - Bethamary Okey

COVID-19: Mu na ji mu na gani ciwon hanji ya kashe Kaninmu - Bethamary Okey

Mawakiyar Najeriya, Bethamary Okey ta bada labarin yadda wani ‘danuwanta na jini mai suna Sylvester, ya rasu a sakamakon kin karbarsa da aka yi a wasu asibitoci a Legas.

Jaridar Punch ta ce Bethamary Okey ta ce tsoron yiwuwar kamuwa da cutar COVID-19 ta sa asibitoci da-dama da ke cikin garin Legas su ka ki karbar jinyar wannan kanin na ta.

A cewar mawakiyar, marigayin ya na fama ne da ciwon hanji tun kafin barkewar annobar Coronavirus. A watan Afrilu wadanda su ke kula da shi su ka bukaci ya canza asibiti.

Tauraruwar ta ce an bukaci su maida maras lafiyan zuwa asibitin koyon aikin jinya na jami’ar Legas da ke garin Idi-Araba, amma likitoci su ki bari a kwantar da shi a kan gadonsu.

Bayan haka ta ce sun garzaya asibitin koyon aiki na jami’ar Legas da ke garin Ikeja, a nan ma dai malaman asibitin sun ji tsoron cewa mara lafiyan ya na dauke da kwayar COVID-19.

KU KARANTA: Najeriya za ta karbo magungunan gargajiyan kasar Madagascar

A karshe aka yi ta zagayawa da wannan Bawan Allah zuwa wasu asibitocin kasuwa amma duk aka rasa inda za a karbe sa. Dole ta sa aka koma gida da shi har ya ce ga garin ku nan.

A cewar ta, a ranar Litinin 4 ga watan Mayu, 2020, marigayin ya shiga wani irin yanayi, har ya sa aka kira ta, ta kuma bukaci malaman addini su yi masa addu’ar domin ya samu sauki.

“Abin da ya sa ‘danuwana ya sallama shi ne asibitoci sun ki bari a karbe sa har a duba sa. Saboda takaici ‘danuwana ya mutu da kimanin karfe 6am na safiyar ranar 5 ga watan Mayu.”

Wani darekta na asibitin LASUTH, Ibrahim Mustafa ya musanya wannan batu, ya ce ba su korar marasa lafiya. Bayan haka likitan ya ce ba su tambayar sakamakon gwajin COVID-19.

Dazu kun ji cewa ruwan wuta ya sa Abubakar Shekau ya fito ya na kuka a wani sabon faifai. Shugaban ‘yan ta’addan ya na neman tsari daga luguden da soji su ke yiwa Boko Haram.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel